'Yan bindiga na neman N10m kudin fansar 'yan uwan ango da amarya da aka sace

'Yan bindiga na neman N10m kudin fansar 'yan uwan ango da amarya da aka sace

- Wasu 'yan bindiga da suka yi garkuwa da wasu masu zuwa biki sun bukaci N10m na fansa

- 'Yan bindigan sun sace mutanen a hanyarsu ta zuwa biki a wani yankin jihar Delta a Najeriya

- Rahotanni sun tabbatar da cewa, ba amarya da angon aka sace ba, wasu ne suke zuwa bikin

Masu garkuwan da suka sace wasu bakin da suka halarci bikin aure a jihar Delta sun bukaci iyalan wadanda abin ya shafa su biya N10m.

Jaridar PUNCH Metro ta tattaro daga majiyoyi na kusa da wadanda aka sacen cewa masu garkuwan sun bude tattaunawa da iyalansu.

Wakilanmu ba su iya tantance yawan mutanen da maharan suka sace ba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari: Okonjo-Iweala ta daga sunan Najeriya a duniya

'Yan bindiga na neman N10m kudin fansar 'yan uwan ango da amarya da aka sace
'Yan bindiga na neman N10m kudin fansar 'yan uwan ango da amarya da aka sace Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

An tattaro cewa an tare bakin akan hanya kuma an sace su a yankin Agbor na Delta, kan hanyar Benin-Asaba, akan hanyarsu ta zuwa bikin aure a ranar Asabar.

Majiyoyi sun bayyana cewa ma'auratan sune ahalin Mista Mordi.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, DSP Onome Onovwakpoyeya, ya shaida wa manema labarai cewa wadanda lamarin ya rutsa da su baƙi ne na bikin aure, ya kara da cewa ba a sace ma'auratan ba.

Ta ce, “Suna tafiya zuwa Benin don wani bikin aure lokacin da aka kai musu hari. Ba sune suke yin aure ba. Sun kasance baƙi.”

KU KARANTA: Kada ku yi tafiya zuwa Kudu maso yamma a yanzu, matasan Arewa ga ‘yan Arewa

A wani labarin, Sufeto-janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya bukaci jami’an rundunar‘ yan sanda ta Najeriya da su jajirce tare da nuna rashin tausayi akan “masu aikata laifuka”, Daily Trust ta ruwaito.

Adamu ya bayyana hakan ne a hedikwatar rundunar, da ke Abuja, yayin kaddamar da wani shiri na musamman na tsaro, wanda aka sanya wa suna “Operation Puff Adder II”, don karfafa yakin da ake yi da ‘yan fashi, satar mutane, fashi da makami da sauran munanan laifuka a kasar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.