Hukumar tsaro ta sojin Najeriya za ta fara daukar aiki a yau Litinin

Hukumar tsaro ta sojin Najeriya za ta fara daukar aiki a yau Litinin

- Hukumar tsaro ta sojin Najeriya ta sanar da bude kafarta ta yanar gizo don daukar sojoji

- Sababbin sojojin da za a dauka an bude rajistarsu a yau ranar Litinin 15 ga watan Fabarairu

- Hukumar ta kuma bayyana abubuwan da masu sha'awar aikin ke bukata don shiga aikin

An fara yin rijistar shiga aikin Soja na Regular Recruit na Sojojin Najeriya a ranar 15 ga watan Fabrairu, in ji rundunar.

Rundunar ta ce rajistar ta yanar gizo za ta kasance a shafinta ga dukkan jama'a da kuma masu sha'awar aikin da suka cancanta, Daily Trust ta ruwaito.

Daukar kuwa zai kasance na 'trade' da kuma 'non-trade' kuma za a dauki maza da mata ne.

KU KARANTA: Okonjo-Iweala za ta zama mace kuma 'yar Afrika ta farko a matsayin DG na WTO a yau

Hukumar tsaro ta sojin Najeriya za ta fara daukar aiki a yau Litinin
Hukumar tsaro ta sojin Najeriya za ta fara daukar aiki a yau Litinin Hoto: The Guardian Nigeria
Source: UGC

Abubuwan da ake bukata

1. Masu neman aikin dole su zama 'yan Najeriya kuma sun mallaki katin shaidar dan kasa.

2. Dole ne su kasance ba su da wata hujja game da aikata laifi

3. Hakanan yakamata su sami takardar kammala sakandare tare da ƙarancin izinin wucewa a darusa huɗu a cikin zaman jarrabawa ba fiye da zama biyu ba.

4. Wadanda ke nema a matsayin 'trade' maza ko mata dole ne su sami gwajin sana'a ko takardar shaidar City Guild.

5. Masu neman aikin ana sa ran basu gaza shekaru 18 ba kuma baza su wuce 22 ba.

6. Dole ne masu nema a fannin 'trade' maza ko mata ba zasu zama kasa da shekaru 22 ba.

KU KARANTA: FCTA za ta rushe wasu gidajen rawa 2 saboda karya dokar COVID-19

A wani labarin, Sojojin Najeriya sun samu kashe mayaƙan Boko Haram 81 a dajin Sambisa. Sai dai sun rasa soja daya a wani harin nakiya, BBC Hausa ta ruwaito.

Kafar yaɗa labarai ta PRNigeria ta ruwaito cewa a yayin tserewa mayaƙan sun lalata gidaje tare da kona wasu. Sojojin dai sun tarwatsa ƙauyukan ƴan ta'addar da damma a yankin garin Bello da Kwoche da Lawanti da Alfa Bula Hassan da Alfa Cross da dai sauransu.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel