Makiyaya da AK-47: Baka cancanci zama gwamna ba, Akeredolu ga gwamnan Bauchi

Makiyaya da AK-47: Baka cancanci zama gwamna ba, Akeredolu ga gwamnan Bauchi

- Gwamnan jihar Ondo ya caccaki gwamnan jihar Bauchi sakamakon goyon bayan makiyaya

- Ya bayyana goyon bayan rike bindiga ga makiyaya a matsayin tunzura aikata ta'addanci

- Ya kuma bayyana cewa masu hali irin na gwamnan basu cancanci aikin gwamnati ba

Don bayyana goyon baya ga makiyaya wadanda ke dauke da bindigogin AK-47, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya fuskanci shan suka daga mutane a duk bangarorin siyasa wadanda suka bayyana kalaman nasa da "rashin kulawa da tunzura jama'a."

Mohammed ya ba da hujjar daukar muggan bindigogi da makiyaya ke yi da nufin kare kai daga barayin shanu da sauran barazana, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Yamma kuma gwamnan jihar Ondo, Mista Rotimi Akeredolu, ya bayyana gwamnan na Bauchi a matsayin mai tayar da hankali kuma wanda bai cancanci mukamin gwamnati ba.

KU KARANTA: Obasanjo ga shugabannin Afirka: Kada ku bari COVID-19 ta hana aiwatar da AfCFTA

Makiyaya da AK-47: Baka cancanci zama gwamna ba, Akeredolu ga gwamnan Bauchi
Makiyaya da AK-47: Baka cancanci zama gwamna ba, Akeredolu ga gwamnan Bauchi Hoto: Policy and Legal Advocacy Center
Source: UGC

Da yake magana ta bakin Kwamishinansa na yada labarai da wayar da kai, Mista Donald Ojogo, Akeredolu ya nuna takaicin sa kan kalaman da aka jingina ga gwamnan Bauchi, yana mai bayyana shi a matsayin abin ban tsoro da takaici.

Gwamnan yace yana da yakinin cewa gwamnan bai fadi wadancan kalamai ba, idan kuma ya tabbata ya fadi haka, a cewarsa hakan nufin cewa,

"gwamnan jihar Bauchi ya ayyana a madadin Gwamnatin Tarayya, Dokar Zartarwa wanda a yanzu ya ba dukkan ‘yan Nijeriya, makiyaya baki daya damar daukar haramtattun bindigogi kamar bindigogi don kare kai.

”Wannan shi ne ainihin abin da Gwamnan ya yi kuma ya nuna ta hanyar halayensa wanda ke nuna cewa ko wasu 'yan Najeriya suna so ko ba sa so, makiyaya dole ne su dauki AK-47 don kare kansu." in ji Akeredolu.

Gwamnan, wanda ya kuma bayyana bayanin a matsayin magana mara ma'ana da tunzura mutane.

“Gwamnan Bauchi ya nuna halayyarsa da dabi'unsa ya kai mu mataki na gaba kan turbar rashin tsari. Bai cancanci mukamin gwamnati ba, mutanen masu irin wannan hali ba su dace da aikin gwamnati ba," in ji shi.

KU KARANTA: Buhari yana kokarin gyara matsalolin Najeriya, in ji Amb Yabo

A wani labarin, Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeder’s Association of Nigeria (MACBAN) ta shawarci Gwamnatin Tarayya da ta kyale kowane dan Najeriya ya mallaki bindigogi don kare kansa duba da kalubalen tsaro a kasar.

Kungiyar ta yi wannan kiran ne yayin da take mayar da martani a kan kalaman da Gwamnan Bauchi, Sen. Bala Mohammed, ya yi cewa makiyaya suna dauke da bindigogi ne kawai don kare kansu.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel