Gwamna Zulum ya yiwa wani likita Bayarbe kyautar mota da biyansa kudi N13.9m

Gwamna Zulum ya yiwa wani likita Bayarbe kyautar mota da biyansa kudi N13.9m

- Gwamnan jihar Borno ya sharewa wani likita a jihar hawaye da kyautar mota mai tsada

- Gwamnan ya kuma bada umarnin a saki kudaden da likitan ke bin gwamnatin jihar ta Borno

- Ya kuma bada umarnin daukar 'yar likitan aiki a ma'aikatar farar hula ta jihar Borno

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da biyan naira miliyan 13.9 da kyautar mota ga wani likita mai shekaru 65 daga jihar Ogun.

Likitan shine wanda ke zaune a cikin Babban Asibitin da ke Monguno kuma ya ci gaba da kula da marasa lafiya har ma lokacin da garin ya fuskanci mummunar barazanar kungiyar Boko Haram, The Nation ta ruwaito.

Likitan, Dakta Isa Akinbode, ya kammala karatun sa ne a Jami’ar Maiduguri ya kuma shiga aikin Gwamnatin Jihar ta Borno, inda ya yi aiki na tsawon shekaru 22 kafin ya yi ritaya a shekarar 2016 a babban asibitin Monguno.

KU KARANTA: Gwamnatin Saudiyya ta rufe wasu masallatai saboda saba dokar Korona

Gwamna Zulum ya yiwa wani likita Bayarbe kyautar mota da biyansa kudi N13.9m
Gwamna Zulum ya yiwa wani likita Bayarbe kyautar mota da biyansa kudi N13.9m Hoto: Tribune Online
Asali: UGC

Bayan ya yi ritaya, likitan, duk da rahotanni da ke cewa sau daya kungiyar Boko Haram ta sace shi kuma ta sake shi a Monguno, ya ci gaba da kasancewa a Babban Asibitin da ke Monguno don yin hidimomin lafiya kyauta.

Sannan Gwamna Kashim Shettima, a lokacin daya kai ziyara zuwa Monguno, ya umarci jami’an Ma’aikatar Lafiya ta jihar da su sa Akinbode a matsayin ma’aikacin kwangila.

Dangane da hanyoyin gudanar da aiki, jami’ai a ma’aikatar a Maiduguri, duk da haka, sun jinkirta kafa kwangilar likitan, duk da cewa ya ci gaba da aiki.

Shekaru biyar bayan haka, Gwamna Zulum, a ranar Juma'a, ya ba da umarnin a biya likitan hakkokinsa kowane wata.

Gwamnan ya kuma gabatar da kyautar Toyota Highlander a matsayin kyauta ga Dakta Akinbode saboda ayyukansa ga mutanen da suka karbi bakuncin mutanen Borno.

“Wadannan (mutane kamar Dr Akinbode) su ne ire-iren mutanen da suke bukatar a karfafa su. Yana zaune a Monguno duk da matsalolin tsaro." In ji Zulum.

Gwamna Zulum ya kuma amince da daukar ‘yar Dr Akinbode, wacce ta karanci ilimin mulki a jami’ar Maiduguri, zuwa ma’aikatan farar hula na jihar Borno.

KU KARANTA: Mutane da dama sun mutu a rikicin Hausawa da Yarbawa a jihar Oyo

A wani labarin, Majalisar masu harhada magunguna a Najeriya ta ce jihohin Yobe da Zamfara dukkansu biyun na da kantunan magunguna guda 22 ga kuma karancin kwararrun likitocin magunguna.

Majalisar ta ce sabanin yadda mutane da yawa za su yi tunani, yawan matsalar rashin tsaro a Arewa ba shi da nasaba da halin da ake ciki.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.