Buhari yana kokarin gyara matsalolin Najeriya, in ji Amb Yabo
- Wani jakadan Najeriya da aka nada a baya-bayan nan ya yabawa shugaba Buhari
- Ya bayyana cewa shugaba Buhari yana aiki tukuru don magance matsalolin Najeriya
- Ya kuma kirayi 'yan Najeriya da su ci gaba da goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari
Sabon jakadan Najeriya da aka nada a Jordan, Faruk Malami Yabo ya tabbatar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari na aiki kai tsaye don gyara matsalolin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.
Da yake magana a mahaifarsa ta Yabo bayan sake jaddada rajistarsa ta zama dan jam'iyyar APC a ranar Lahadi, ya ce, shugaban ya gaji tarin matsaloli wadanda za su dauki lokaci kafin a magance su.
“Kun san barna tana faruwa ne cikin sauki amma sake ginawa dole sai a hankali.
“Lokacin da wannan gwamnatin ta hau, akwai kalubale da yawa da suka hada da tawaye da sauran nau’ikan laifuka; cin hanci da rashawa ya kasance a matakin koli kuma tattalin arzikinmu ya kasance a sume.
KU KARANTA: Kada ku yi tafiya zuwa Kudu maso yamma a yanzu, matasan Arewa ga ‘yan Arewa
"Amma yanzu mun ga raguwar tawaye da cin hanci yayin da gwamnati ke aiki tukuru don magance wasu matsalolin," in ji shi.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da ba da goyon baya da yi wa gwamnati addu’a, yana mai bayar da tabbacin cewa sabuwar hanyar da gwamnatin tarayya ta bi za ta kawo karshen matsalar tsaron da muke ciki.
Saboda haka, ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari game da kawo abubuwan ci gaba a duk fadin kasar da kuma shirin saka jari wanda ya karfafawa 'yan Najeriya da yawa.
Yabo ya kuma bukaci mambobin jam'iyyar APC da su kiyaye da hankali da kuma da'a.
Ya yi watsi da zancen da ake yi cewa, an nada shi Jakada ne don ya hana shi neman kujerar gwamna a karkashin jam'iyyar a 2023.
A kan abin da kasar za ta tsammata daga gare shi a Jordan, ya ce zai yi aiki don dorewa da inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
KU KARANTA: A baiwa 'yan Najeriya damar mallakar bindiga, in ji kungiyar miyetti Allah
A wani labarin, Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya shawarci ‘yan siyasan Najeriya da kada su dauki zabe a matsayin juyin mulki ko yaki, a’a su hadu su goyi bayan duk wanda ya samu nasara, Daily Trust ta ruwaito.
Da yake magana a Yenegoa, babban birnin jihar Bayelsa yayin bikin nuna godiya / bikin cika shekara daya da Gwamna Douye Diri na mulki, Jonathan ya kuma shawarci wadanda ke cikin siyasa da kada su yi riko da dacin rai.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng