Obasanjo ga shugabannin Afirka: Kada ku bari COVID-19 ta hana aiwatar da AfCFTA

Obasanjo ga shugabannin Afirka: Kada ku bari COVID-19 ta hana aiwatar da AfCFTA

- Tsohon shugaban kasar Najeriya ya shawarci shugabannin Afrika kan shirin AfCFTA

- Ya jaddada cewa bai kamata cutar Korona ta zama dalilin rugujewar shirin ba baki daya

- Ya kuma shawarcesu kan ci gaba da shirin yadda idan aka samu saukin Korona a cigaba cikin sauki

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya fadawa shugabannin kasashen Afirka da su kalli annobar COVID-19 a matsayin tursasawa ba cikas ga cikakken aiwatar da yankin Kasuwancin Kasashen Afirka (AfCFTA) ba.

Obasanjo ya ce jinkirin cikakken aiwatarwa sakamakon barkewar annobar ya kamata ya ba shugabanni “damar yin karin aiki tukuru wanda ke bukatar dan lokaci ta yadda idan daga karshe za mu fara aiki mu kasance cikin shiri da kuma yin hakan a cikakken karfi.”

Ya kuma gargadi kasashen Afirka da kada su bari harkar noma da bangarorin masana'antu su tabarbare saboda cutar COVID-19, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: A baiwa 'yan Najeriya damar mallakar bindiga, in ji kungiyar miyetti Allah

Obasanjo ga shugabannin Afirka: COVID-19 ba za ta hana aiwatar da AfCFTA
Obasanjo ga shugabannin Afirka: COVID-19 ba za ta hana aiwatar da AfCFTA Hoto: Vanguard News
Source: UGC

Wata sanarwa da mai taimaka wa Obasanjo na yada labarai, Kehinde Akinyemi a ranar Lahadi, a Abeokuta, ya nakalto shi ya yi magana lokacin da ya bayyana a cikin wannan makon na ACCORD 2021 jerin Rikicin COVID-19 da kuma mafita.

Obasanjo, a cikin sallamarsa, ya gabatar da hujja ne game da dogaro da kai na Afirka da kuma samo hanyoyin da za a bi na gida don nahiyar ta farfado musamman daga lalacewar tattalin arziki da COVID-19 ta haifar.

Ya ce “A lokacin da muke duban kasuwanci, yana da muhimmanci a bayyane a fahimtarmu cewa COVID-19 ya jinkirta ne kawai, amma ba a karkatar da shi ba, aiwatar da Yankin Kasuwancin Nahiyar Afirka (AfCFTA).

Ya kuma jaddada cewa bai dace a zauna ba tare da duba zuwa ga tsarin na AfCFTA ba.

“Duk da haka, dole ne mu yi la’akari da, mu kuma fahimci gaskiyar cewa wasu fannoni da suka shafi cikakken aiki da AfCFTA na buƙatar tuntuɓar jiki, wanda ba zai iya faruwa a wannan matakin ba saboda matakan da aka sanya don magance COVID-19.

KU KARANTA: Kada ku yi tafiya zuwa Kudu maso yamma a yanzu, matasan Arewa ga ‘yan Arewa

A wani labarin, Gwamnatin Saudiyya ta rufe wasu masallatai bayan an samu cikin masu ibada da suka kamu da cutar korona, BBC Hausa ta ruwaito.

Ma’aikatar lamurran addini ta kasar ta ce masallatai biyar ne aka rufe, hudu a Riyadh babban birnin kasar da kuma daya da ke kusa da kan iyaka a yankin arewaci, kamar yadda kamfanin dillacin labaran kasar ya ruwaito.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel