A baiwa 'yan Najeriya damar mallakar bindiga, in ji kungiyar miyetti Allah

A baiwa 'yan Najeriya damar mallakar bindiga, in ji kungiyar miyetti Allah

- Kungiyar miyetti Allah ta bukaci gwamnatin tarayya da ta bar 'yan Najeriya su mallaki bindiga

- Kungiyar ta yi wannan furuci ne saboda rashin kula da gwamnati ke yi a fannin tsaron jama'a

- Kungiyar ta kuma goyi bayan gwamnan jihar Bauchi da furucinsa na baya kan makiyaya

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeder’s Association of Nigeria (MACBAN) ta shawarci Gwamnatin Tarayya da ta kyale kowane dan Najeriya ya mallaki bindigogi don kare kansa duba da kalubalen tsaro a kasar.

Kungiyar ta yi wannan kiran ne yayin da take mayar da martani a kan kalaman da Gwamnan Bauchi, Sen. Bala Mohammed, ya yi cewa makiyaya suna dauke da bindigogi ne kawai don kare kansu.

Gwamna Mohammed ya sha suka sosai bayan goyon bayan makiyaya na yin amfani da AK-47 don kare kansu daga barayin shanu.

Shugaban kungiyar ta MACBAN na jihar Bauchi, Alhaji Sadiq Ibrahim Ahmed, ya fadawa jaridar The Nation a ranar Lahadi cewa babu wani abin damuwa game da tsayuwar Gwamnan tunda bai ce makiyaya su je su haddasa rikici da shi ba.

KU KARANTA: Gwamnatin Saudiyya ta rufe wasu masallatai saboda saba dokar Korona

A baiwa 'yan Najeriya damar mallakar bindiga, in ji kungiyar miyetti Allah
A baiwa 'yan Najeriya damar mallakar bindiga, in ji kungiyar miyetti Allah Hoto: The Guardian Nigeria
Source: UGC

A cewarsa, tunda Gwamnatin Tarayya ba za ta iya kare ‘yan kasa ba, yana da kyau kowane dan kasa ya kare kansa daga 'yan fashi.

Ya ce "Gwamnati ta zama mai rikon sakainar kashi. Hakan yasa Bafulatani ya zama saniyar ware a kasarsa.

“Dukkanin dukiyarsa ta gurgunta ga satar barayin shanu. Me kuke tsammanin ya yi?

“Kowa ya kare kansa, kowa ya dauki makami. Kada ku bari 'yan fashi su zo su lalata ku, su kashe ku, su kashe danginku saboda mutane ƙalilan ba za su iya tsoratar da kowa ba.”

“Ba zan zargi Gwamna Bala Mohammed ba game da maganarsa, ya yi daidai. Tunda bai ce makiyaya su je su tayar da hargitsi ba.

“Babu wanda ya aibata Gwamnan Benue, Ortom lokacin da ya ce makiyaya su bar jiharsa. Don haka me ya sa suke sukar gwamnan Bauchi?”

KU KARANTA: Yobe da Zamfara na da kasa da kantunan magani 22 a hade, in ji PCN

A wani labarin, Saleh Alhassan, shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Haure na kasa, ya ce kungiyar a shirye ta ke ta mayar da martani kan kashe mambobin ta da ake yi a fadin Nigeria.

A tattaunawar sa da jaridar The PUNCH, Alhassan ya yi ikirarin cewa da yawan makiyayan da ake kai masu farmaki da kashe su a fadin kasar, mutane ne da basu ji ba basu gani ba.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel