Osinbajo yayi Allah wadai da harin da ake kaiwa yan Arewa a Shasha

Osinbajo yayi Allah wadai da harin da ake kaiwa yan Arewa a Shasha

- Mataimakin shugaban kasar Najeriya yayi Allah wadai da rikicin da ke faruwa a jihar Oyo

- Mataimakin shugaban ya siffanta hakan da abin kunya tsakanin Hausawa da Yarbawa

- A cewarsa, kasuwar Sasha kasuwace da Hausawa ke rayuwa tare da Yarbawa tsawon shekaru

Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a ranar Lahadi ya la’anci rikicin kabilanci da ya faru a Shasha a Ibadan, Jihar Oyo yana mai bayyana shi a matsayin abin takaici, Daily Trust ta ruwaito.

Osinbajo ya ce shahararriyar kasuwar Shasha alama ce ta hadin kai shekaru da dama.

Da yake magana a Legas lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya zuwa gidan marigayi Lateef Jakande da ke Ilupeju, mataimakin shugaban kasan ya ce:

“Shekaru da dama, 'yan kasuwa daga Arewa sun yi kasuwanci da ’yan uwansu daga Kudu maso Yamma kuma sun zauna lafiya har ma sun yi aure. Shasha wakiliyar hadin kai ne.”

KU KARANTA: Buhari yana kokarin gyara matsalolin Najeriya, in ji Amb Yabo

Osinbajo yayi Allah wadai da rikicin Shasha, inji shi Kasuwa na nufin Hadin Kai
Osinbajo yayi Allah wadai da rikicin Shasha, inji shi Kasuwa na nufin Hadin Kai Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Osinbajo ya yi gargadi game da bai wa rikicin sunan rikice-rikicen kabilanci, yana mai cewa:

“Rashin jituwa da ke tasowa tsakanin mutane ko kuma idan wani laifi ya faru da wani a kan daya dole ne mu tabbatar mun gan shi yadda abin yake, a matsayin laifi, wanda dole ne a hukunta shi bisa doka. Ba rikicin kabilanci ba.

Osinbajo ya kuma gargadi daidaikun mutane game da daukar doka a hannunsu, yana mai cewa,

“Kowane dan Najeriya yana da damar da kundin tsarin mulki ya ba shi na rayuwa, aiki da jin dadin rayuwarsa cikin aminci, zaman lafiya a karkashin doka.
“Hakkin gwamnati ne ta hanyar 'yan sanda da sauran jami’an tsaro su kame tare da gurfanar da duk wani mutum da ya aikata laifi kan wani dan kasar nan. Hakkin dan kasa ne ya taimakawa ‘yan sanda don gano masu laifin.
"Ina kira ga dukkan shugabannin al'umma da su yi aiki tare don kiyaye zaman lafiya da 'yan uwantaka da mutanenmu daga sassa daban-daban na kasar da suke zaune a kasuwar Shasha tsawon shekaru da dama."

KU KARANTA: Obasanjo ga shugabannin Afirka: Kada ku bari COVID-19 ta hana aiwatar da AfCFTA

A wani labarin, Kungiyar Matasan Arewacin Najeriya (NYCN) ta nuna damuwarta kan yawan hare-haren da ake zargin ‘yan Arewa da kai wa, musamman harin baya-bayan nan a kasuwar Sasha ta karamar Hukumar Akinyele da ke Oyo, The Nation ta ruwaito.

Wata sanarwa daga kakakinta, Mock Kure, ta ce: “Hankalin Majalisar Matasan Arewacin Najeriya ya karkata ne kan barna da ake yi wa 'yan Arewa, musamman a Kasuwar Sasha ta Karamar Hukumar Akinyele, Jihar Oyo, Kudu maso Yammacin Najeriya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.