Hausawa 3,000 sun fake a gidan Sarki, an birne gawa 11 a kashe-kashen Jihar Oyo

Hausawa 3,000 sun fake a gidan Sarki, an birne gawa 11 a kashe-kashen Jihar Oyo

- Mutane kusan 20 ake zargin an kashe a rikicin da ya barke a yankin Shasha

- Jama’a su na cigaba da fakewa a gidan Sarki da ma’aikatar gona ta Ibadan

- Gwamnan Jihar Oyo, Oluseyi Makinde da Rotimi Akeredolu sun kai ziyara

Akalla mutane 11 aka birne a ranar Lahadi, 14 ga watan Fubrairu, 2021, bayan rikicin da aka yi tsakanin Hausawa da Yarbawa a kasuwar Shasha, Oyo.

Daily Trust ta fitar da rahoto cewa wannan rigima da ta barke a karamar hukumar Akinyele, jihar Oyo, ta ci ran mutane kimanin 20 a karshen makon nan.

Hausawa kusan 5, 000 da su ke kasuwanci da kuma matansu da kananan yara sun fake a gidan Sarkin Shasa, Alhaji Haruna Maiyasin, saboda gudun hari.

Wasu mutanen kuma sun samu mafaka a ma’aikatar aikin gona ta IITA da ke garin Ibadan.

KU KARANTA: An ba mutanen Arewa shawara su guji zuwa Kudu a yanzu

Sarkin Shasa, Alhaji Haruna Maiyasin ya yi magana da ‘yan jarida, ya ce an yi wa mutane 11 suturam za a birne su, bayan an hallaka su a rikicin da aka yi.

‘Za ku iya jin karan mutane, su na nan har yanzu." Alhaji Maiyasin ya fada wa Daily Trust a waya cewa mutanen da su ke zaune cikin gidansa sun haura 3, 000.

Wata majiyar ta tabbatar da cewa mutanen da aka birne a Akinyele sun haura 20 a karshen makon nan. Kowane bangare ya rasa mutane a wannan rikici da aka yi.

Ragowar gawan mutane akalla 8 da su ka rasu, su na hannun dakarun ‘yan sanda na reshen Shasha.

KU KARANTA: An kona motoci da abinci a jihar Oyo

Hausawa 3,000 sun fake a gidan Sarki, an birne gawa 11 a kashe-kashen Jihar Oyo
Gwamnan Jihar Oyo Hoto; Amotekun
Source: Facebook

Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun tura jami’ai zuwa gidan Sarkin Hausawa da ke Mokola a yankin Sabo, domin tabbatar da cewa rigimar ba ta cigaba da barke wa ba.

Jama’a sun yi wa gwamna Rotimi Akeredolu da Seyi Makinde ihu yayin da su ka ziyarci Sasha, ana zarginsu da zuwa a makare bayan an kashe mutane rututu.

Garba Shehu ya fitar da jawabi a jiya, ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba za ta zura ido wasu gungun mutane su tada wutar rikici a kasar nan ba

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawari cewa ba zai bari wata kungiyar addini ko kuma kabila ta jawo fada da mugun rikicin kiyayya da juna a Najeriya ba.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel