Rikicin Hausawa da Yarbawa: An kone wasu motoci makare da kayan abinci

Rikicin Hausawa da Yarbawa: An kone wasu motoci makare da kayan abinci

- Rikici tsakanin Hausawa da Yarbawa a yankinkudancin Najeriya na kara ta'azzama

- Bayan sanya dokar taba baci a jihar, ana ci gaba da kone-konen motoci a kan manyan hanyoyi

- Hotunan wasu manyan motoci makare da kayan abinci da aka cinna wa wuta sun bazu a kafofin sada zumunta

A ci gaba da tashin hankalin da ya ke ta faruwa tsakanin Hausawa da Yarbawa a yankin kudancin Najeriya, wasu 'yan daba suna ta kone-konen motoci da kan manyan hanyoyi.

Daily Trust ta gano. hotunan wasu motoci biyu makare da kayan abinci na miliyoyin nairori wadanda ‘yan daba suka cinna wa wuta a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan bayan rikici tsakanin Hausawa da Yarbawa mazauna ranar Juma’a.

KU KARANTA: Yobe da Zamfara na da kasa da kantunan magani 22 a hade, in ji PCN

Rikicin Hausawa da Yarbawa: An kone wasu motoci makare da kayan abinci
Rikicin Hausawa da Yarbawa: An kone wasu motoci makare da kayan abinci Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Hotunan suna ta yawo a kafafen sada zumunta, yayin da a wasu rahotanni na jaridar Premium Times ke bayyana cewa wasu tsagerun Yarbawa na tare motoci a kan manyan hanyoyi tare da tambayar mutane asalin kabilarsu.

Hakan ya biyo bayan wani tashin hankali ne da faru tsakanin wasu mutane biyu a kasuwar Sasa dake jihar Oyo a ranar Juma'a da ta gabata.

Hakan ya kuma jawo sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Rikicin Hausawa da Yarbawa: An kone wasu motoci makare da kayan abinci
Rikicin Hausawa da Yarbawa: An kone wasu motoci makare da kayan abinci Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnatin Saudiyya ta rufe wasu masallatai saboda saba dokar Korona

A wani labarin, Mutane da dama sun rasa rayukansu bayan wani rikici da ya faru sanadiyyar kisan wani mai gyaran takalma da wani mai dakon kaya ya yi a kasuwar Sasha, Ibadan, Jihar Oyo, ya rikide zuwa rikicin kabilanci.

An tabbatar da cewa wanda aka kashen ya mutu ne a asibiti a safiyar ranar Juma’a, lamarin da ya haifar da rikici tsakanin al’ummar Hausawa da Yarbawa, inda Yarbawan ke kokarin daukar fansar mutuwar dan nasu.

Cikin ‘yan awanni, rikicin ya bazu wajen kasuwar, yayin da al’ummar Hausawa da Yarbawa a karamar Hukumar Akinyele, inda kasuwar take, suka afkawa juna.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.