Kashe-kashe: A karshe Buhari ya yi magana da babbar murya, ya sha alwashin kare ran kowa

Kashe-kashe: A karshe Buhari ya yi magana da babbar murya, ya sha alwashin kare ran kowa

- Fadar Shugaban kasa ta yi magana game da rikicin da ya barke a Oyo

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan Bayin Allah

- Buhari ya ce Gwamnatinsa ba za ta yarda a auka wa wasu al’umma ba

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawari cewa ba zai bari wata kungiyar addini ko kabila ta jawo fada da rikicin kiyayya da juna a Najeriya ba.

Shugaban kasar ya fitar da jawabi ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, a ranar Lahadi, 14 ga watan Fubrairu, 2020 ta shafin Twitter.

Fadar shugaban kasar ta fito ta yi tir da rikicin da wasu bangare na kasar su ke neman su tada a Najeriya.

Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da abubuwan da ke faru wa a kudancin Najeriya inda ake hallaka mutanen wasu kabila, a garin Shashsa, jihar Oyo.

KU KARANTA: Kashe-kashe: Matakin da za mu dauka - NSA

“Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashi gwamnatinsa za ta kare dukkan kabilu da addinai; masu rinjaye ko marasa rinjaye, kamar yadda tsarin mulki ya daura mata nauyi.”

Jawabin ya cigaba: “Shugaban kasa ya na gargadi cewa gwamnatinsa ba za ta bari wasu kungiyoyin addinai ko kabilu su tado da rikici da ta’adi a kan sauran jama’a ba.”

A jawabin da ya fitar jiya da daddare, Mai girma shugaban kasar ya tabbatar da cewa zai kawo karshen wannan kashe-kashe domin ganin abin bai yadu zuwa sauran wurare ba.

“(Buhari) ya yi kira ga shugabannin addini da gargajiya, har da gwamnoni da zababbun shugabanni a kasar, su hada kai da gwamnatin tarayya na ganin an samu zaman lafiya.”

KU KARANTA: Boko Haram: ‘Yan ta’adda sun yi mafaka a wasu Jihohin Arewa

Kashe-kashe: A karshe Buhari ya yi magana da babbar murya, ya sha alwashin kare ran kowa
Shugaban Najeriya Buhari Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Hakan na zuwa ne bayan kashe-kashen da aka yi sun jawo rashin rayukar Hausawa da dukiyoyinsu a Oyo.

Kwanakin baya kun ji cewa kungiyar Miyetti Allah ta amince da rajistar makiyaya, ta bukaci a raba masu kati ta yadda za a rika banbance nagari da miyagu.

Shugabannin Fulani sun sha alwashin bankado duk wani Makiyayi da ya ke yawo da makamai.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), na reshnen Ekiti, Adamu Abache, ya goyi bayan matakan da gwamnati ta zo da su.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng