Yobe da Zamfara na da kasa da kantunan magani 22 a hade, in ji PCN

Yobe da Zamfara na da kasa da kantunan magani 22 a hade, in ji PCN

- Kungiyar masu harhda magunguna Najeriya ta bayyana karancin shagunan magani a jihohin arewa

- Kungiyar ta bayyana haka a cikin wani bincike da ta gudanar na adadin shagunan magani a aksar

- Zamfara da jihar Yobe an bayyana su ne masu mafi karancin shagunan magani da kwararrun ma'aikatan lafiya

Majalisar masu harhada magunguna a Najeriya ta ce jihohin Yobe da Zamfara dukkansu biyun na da kantunan magunguna guda 22 ga kuma karancin kwararrun likitocin magunguna.

Majalisar ta ce sabanin yadda mutane da yawa za su yi tunani, yawan matsalar rashin tsaro a Arewa ba shi da nasaba da halin da ake ciki.

Kwamitin PCN yayi magana game da binciken da aka buga a cikin Journal of Pharmaceutical Policy and Practice.

Binciken, mai taken, An Analysis of Pharmacy Workforce Capacity in Nigeria, ya bayyana cewa akasarin ma’aikatan hada magungunan da ke da lasisi a kasar suna jihar Legas, mai masana magunguna 3,661; da Babban Birnin Tarayya, 1,540.

KU KARANTA: Bai kamata 'yan siyasa suke ganin zabe a matsayin juyin mulki ba, in ji Jonathan

Yobe da Zamfara na da kasa da kantunan magani 22 a hade, in ji PCN
Yobe da Zamfara na da kasa da kantunan magani 22 a hade, in ji PCN Hoto: Nigerian Infopedia
Source: UGC

Sai dai, jihohin Yobe da Zamfara su ke da mafi karancin masana magunguna (20 da 22 bi da bi).

Saboda haka, da yake magana da PUNCH HealthWise, Jami’in Hulda da Jama’a na PCN, Dokta Peter Illiya, ya ce, PCN na iya bayyana cewa jihohin Yobe, Zamfara da Jigawa a hade ba su da wuraren magunguna da suka haura 22.

“Bambancin yawan kantunan da masu sayar da magunguna kansu ba zai iya zama mai yawa ba. Gwargwado, daidai yake. Mu ne masu kula da bayanai a PCN. Yobe, Zamfara kuma, ina ji, Jigawa da kuka ambata ba su da da wuraren sayar da magunguna da suka haura 22.

“Zan iya fada muku a sarari cewa Yobe ba ta da har zuwa shagunan sayar da magani guda biyar a dukkanin yankunanta zuwa sadda muke maganar nan.

“Jigawa tana da guda biyu a lissafinmu na karshe, kuma ya kamata Zamfara ta haura ta hakan.

"Duk da haka, Lagos da Abuja suna ci gaba da rike matsayinsu a matsayin manyan cibiyoyin masu bada magunguna da wuraren bada magunguna," in ji mai yin hoton na PCN.

KU KARANTA: 'Yan majalisu na duba kudirin dakatar da 'yan jaridun da basu da digiri daga aiki

A wani labarin, Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), ta gano wata ma'ajiya ta tabar wiwi a yankin karamar hukumar Guma ta jihar Benue, Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun hukumar, Jonah Achema, ya fadi haka a ranar Asabar a Abuja cewa hukumar ta kuma kama wata babbar motar daukar muggan kwayoyi a jihar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel