Gwamnatin Saudiyya ta rufe wasu masallatai saboda saba dokar Korona
- A kokarin kare yaduwar cutar Korona, masarautar kasar Saudiyya ta sake garkame wasu masallatai
- Rohoto ya bayyana cewa, an samu wasu da suke dauke kwayar cutar a cikin masallatan
- Gwamnatin zuwa yanzu ta garkame masallatai sama to, yayin da kuma take ci gaba da sanya dokoki ga wadanda aka bude
Gwamnatin Saudiyya ta rufe wasu masallatai bayan an samu cikin masu ibada da suka kamu da cutar korona, BBC Hausa ta ruwaito.
Ma’aikatar lamurran addini ta kasar ta ce masallatai biyar ne aka rufe, hudu a Riyadh babban birnin kasar da kuma daya da ke kusa da kan iyaka a yankin arewaci, kamar yadda kamfanin dillacin labaran kasar ya ruwaito.
KU KARANTA: Da yawan masu zanga-zangar #EndSARS 'yan damfara ne da barayi, ministan tsaro
asallatai kimanin 57 yanzu Saudiyya ta rufe cikin mako daya, yayin da aka bude 44 daga cikinsu bayan an yi masu feshi da kuma gindaya sharadda ga masallata.
Gwamnatin ta bukaci mutane su kiyaye sharuddan kwayar cutar korona tare da bayar da rahotanni kan duk masallacin da ya saba dokokin.
KU KARANTA: FG ga gwamnoni: Akwai hanyoyi da yawa da zaku iya bi don karar da 'yan ta'adda
A wani llabarin, Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), Alhaji Zikrullah Hassan, a ranar Lahadin da ta gabata ya shawarci ‘yan Nijeriya da su 'yantar da gwamnati daga shiga harkar kudi a aikin Hajji, Daily Trust ta ruwaito.
Alhaji Hassan ya ba da wannan shawarar ne a wata addu’a ta musamman da al’ummar Musulmin Kudu maso Yammacin Nijeriya (MUSWEN) suka shirya domin girmama shi bisa nadin da aka yi masa a matsayin shugaban NAHCON.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng