Mutane da dama sun mutu a rikicin Hausawa da Yarbawa a jihar Oyo

Mutane da dama sun mutu a rikicin Hausawa da Yarbawa a jihar Oyo

- An kashe kimanin Hausawa 10 a wata kasuwa dake jihar Oyo a kudancin Najeriya

- Talatin daban sun tsere yayin harin da Amotekun ta kai wa kasuwar ta Hausawa

- Gwamnatin jihar ta kulle kasuwar tare da sanya dokar hana fita a yankin kasuwar

Mutane da dama sun rasa rayukansu bayan wani rikici da ya faru sanadiyyar kisan wani mai gyaran takalma da wani mai dakon kaya ya yi a kasuwar Sasha, Ibadan, Jihar Oyo, ya rikide zuwa rikicin kabilanci.

An tabbatar da cewa wanda aka kashen ya mutu ne a asibiti a safiyar ranar Juma’a, lamarin da ya haifar da rikici tsakanin al’ummar Hausawa da Yarbawa, inda Yarbawan ke kokarin daukar fansar mutuwar dan nasu.

Cikin ‘yan awanni, rikicin ya bazu wajen kasuwar, yayin da al’ummar Hausawa da Yarbawa a karamar Hukumar Akinyele, inda kasuwar take, suka afkawa juna.

KU KARANTA: FG ga gwamnoni: Akwai hanyoyi da yawa da zaku iya bi don karar da 'yan ta'adda

Mutane da dama sun mutu a rikicin Hausawa da Yarbawa a jihar Oyo
Mutane da dama sun mutu a rikicin Hausawa da Yarbawa a jihar Oyo Hoto: Inter-Religion
Asali: UGC

Shaidu sun fada wa Premium Times cewa, a kalla, mutane shida sun mutu daga bangarorin biyu a hare-haren ramuwar gayyar. Shaguna da gidaje da dama sun kone yayin da kasuwar ta kasance babu kowa a cikinta.

“Rikicin ramuwar gayya ya haifar da mutuwar aƙalla mutane shida daga ɓangaren Yarabawa da Hausawa.

"A hakikanin gaskiya, mutane da yawa a cikin jama'a sun fantsama don kare lafiyasu,” wani mazaunin garin Akinyele, wanda kawai ya bayyana kansa a matsayin Khalid, ya ce.

A safiyar Asabar, wasu tsagerun Yarbawa sun toshe manyan hanyoyi daban-daban, suna neman fasinjojin da su bayyana kabilunsu.

Da yake magana kan lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Oyo, Olugbenga Fadeyi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sannu a hankali al’amuran na komawa a yankin.

“An tura 'yan sanda masu yawa da kuma na jami’an tsaro don su kwantar da hankula. An kuma tuntubi masu ruwa da tsaki kan lamarin don yin kira ga mutane.”

Domin kawar da karya doka da oda a cikin kasuwar da kewayenta, Gwamna Seyi Makinde a ranar Asabar ya sanya dokar hana fita ba dare ba rana a yankin.

Dangane da rikicin, 'yan Najeriya a shafukan sada zumunta suna ta yada taken #StopKillingNotherners a dandamalin Twitter.

KU KARANTA: 'Yan majalisu na duba kudirin dakatar da 'yan jaridun da basu da digiri daga aiki

A wani labarin, Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ya ce sama da 60% cikin 100% na masu zanga-zangar #EndSARS ba su san dalilin da ya sa suka shiga zanga-zangar ba, jaridar Punch ta tuwaito.

Zanga-zangar #EndSARS ta sake dawowa a Legas ranar Asabar mai taken #OccupyLekkiTollGate, tare da masu zanga-zanga sama da 30, ciki har da Debo Adebayo, wani dan wasan barkwanci da aka fi sani da Mista Macaroni, wanda jami'an tsaro suka kama.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.