Ya kamata 'yan Najeriya su daina tsoma gwamnati a harkar kudin Hajji, in ji NAHCON

Ya kamata 'yan Najeriya su daina tsoma gwamnati a harkar kudin Hajji, in ji NAHCON

- Hukumar aikin hajji ta kasa ta bayyana cewa bai dace 'yan Najeriya su ci gaba da daurawa gwamnati nauyin hajji ba

- Hukumar ta shawarci 'yan Najeriya kan tsarin ajiya na aikin hajji na Bankin Jaiz

- Hakazalika hukumar ta bayyana cewa gwamnati na da bukatun da ya kamata ta sauke sabanin harkar hajji

Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), Alhaji Zikrullah Hassan, a ranar Lahadin da ta gabata ya shawarci ‘yan Nijeriya da su 'yantar da gwamnati daga shiga harkar kudi a aikin Hajji, Daily Trust ta ruwaito.

Alhaji Hassan ya ba da wannan shawarar ne a wata addu’a ta musamman da al’ummar Musulmin Kudu maso Yammacin Nijeriya (MUSWEN) suka shirya domin girmama shi bisa nadin da aka yi masa a matsayin shugaban NAHCON.

Ya ce hukumar ta himmatu wajen ganin aikin hajji ya zama mai sauki da kuma kawar da tsoma gwamnati.

KU KARANTA: Jama'ar gari sun cinna wa wani dan fashi da makami wuta a Yola

Ya kamata 'yan Najeriya su daina tsoma gwamnati a harkar kudin Hajji, in ji NAHCON
Ya kamata 'yan Najeriya su daina tsoma gwamnati a harkar kudin Hajji, in ji NAHCON Hoto: DW News
Source: UGC

Shugaban NAHCON ya ce gabatar da tsarin Ajiya na Aikin Hajji, Cibiyar Horar da Alhazai, da aikin zamanantarwa na aikin hajji da hukumar ke yi da nufin sanya aikin hajji cikin sauki da kuma rage lokacin da za a yi aikin hajjin.

Hassan ya ce gabatar da shirin Ajiya na Aikin Hajji zai taimaka wajen magance kalubalen da kuma kara yawan mutanen da ke zuwa aikin hajji.

“Manufar tanadin aikin hajji ita ce ta yadda talaka zai iya tanadi kadan-kadan tsakanin shekaru biyu zuwa biyar, har sai ya sami damar biyan kudin aikin hajjin.

Hassan ya ce "an mayar da kudin ta hanyar saka hannun jari ta hanyar hadin gwiwarmu da Bankin Jaiz kuma mutane na da damar kara kudadensu a cikin bankin."

Shugaban ya ce wani lokaci zai zo da ba za a bukaci shigar da kudi na gwamnati ba wajen gudanar da aikin hajji.

KU KARANTA: Scholarship: Likitoci mata 47 'yan jihar Kano sun dawo bayan kammala karatu a Sudan

"Ya kamata mu 'yantar da gwamnati daga shigar da kudi a cikin aikin hajji, gwamnati na iya samar da kayan aiki don aikin hajji amma ba ta daukar nauyin mutane zuwa aikin hajji," in ji shi.

A wani labarin, Ana sa ran wasu 'yan Najeriya 802 da suka makale a masarautar Saudiyya za su sauka a Abuja yau da gobe, Daily Trust ta ruwaito.

An tsare su a wurare daban-daban da ake tsare mutane a Saudiyya kan batun kaura ba bisa ka'ida ba.

Sakataren din-din-din na Ma’aikatar Harkokin Waje, Gabriel Aduda, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce za a karbi wadanda za su dawo din ne a Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, ta hanyar jiragen sama biyu na Saudiyya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel