Da yawan masu zanga-zangar #EndSARS 'yan damfara ne da barayi, ministan tsaro

Da yawan masu zanga-zangar #EndSARS 'yan damfara ne da barayi, ministan tsaro

- Ministan tsaro na kasa ya bayyana cewa da yawan masu zanga-zangar #EndSARS barayi ne

- Ministan yace, duk da haka akwai wadanda mutanen kwarai ne kuma mutanen girki

- Ministan ya jaddada cewa gwamnati ba za ta bari wasu bata-gari su hargitsa kasar ba

Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ya ce sama da 60% cikin 100% na masu zanga-zangar #EndSARS ba su san dalilin da ya sa suka shiga zanga-zangar ba, jaridar Punch ta tuwaito.

Zanga-zangar #EndSARS ta sake dawowa a Legas ranar Asabar mai taken #OccupyLekkiTollGate, tare da masu zanga-zanga sama da 30, ciki har da Debo Adebayo, wani dan wasan barkwanci da aka fi sani da Mista Macaroni, wanda jami'an tsaro suka kama.

Amma, an gurfanar da masu zanga-zangar a gaban kotun tafi-da-gidanka a Legas, kuma an bayar da belin su.

Magashi, wanda ya yi magana a ranar Asabar bayan da ya je sake rajistar jam'iyyar APC a Kano, ya yi zargin cewa wasu daga cikin masu zanga-zangar 'yan iska ne da barayi.

KU KARANTA: 'Yan majalisu na duba kudirin dakatar da 'yan jaridun da basu da digiri daga aiki

Da yawan masu zanga-zangar #EndSARS 'yan damfara ne da barayi, ministan tsaro
Da yawan masu zanga-zangar #EndSARS 'yan damfara ne da barayi, ministan tsaro Hoto: FRCN
Asali: UGC

Ya ce, “Akwai babban nauyi na gwamnati, kuma hakan shi ne ta kare kowane dan Najeriya, ko wanene shi. A koyaushe muna yin imanin cewa idan aka ba da hankali, babu wani wakilin gwamnati da zai zauna ya dunkule hannu ba tare da yin wani abu ba.

“Kun san dunbin taron #EndSARS. Fiye da 60% cikin 100% daga cikinsu mutane ne waɗanda ba su ma san dalilin da ya sa suke wurin ba.

"Sun zo ne kawai don su shiga. Wasu daga cikinsu 'yan damfara ne; wasu suna can suna sata. Suna son yin duk abin da suke tunani. Akwai ainihin mutane (daga cikin masu zanga-zangar)."

Ministan ya kara da cewa gwamnati ba za ta kyale "wasu marasa kishin kasa" su hargitsa kasar ta kowane irin rufa-rufa ba.

KU KARANTA: Bai kamata 'yan siyasa suke ganin zabe a matsayin juyin mulki ba, in ji Jonathan

A wani labarin, Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), ta gano wata ma'ajiya ta tabar wiwi a yankin karamar hukumar Guma ta jihar Benue, Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun hukumar, Jonah Achema, ya fadi haka a ranar Asabar a Abuja cewa hukumar ta kuma kama wata babbar motar daukar muggan kwayoyi a jihar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.