FG ga gwamnoni: Akwai hanyoyi da yawa da zaku iya bi don karar da 'yan ta'adda

FG ga gwamnoni: Akwai hanyoyi da yawa da zaku iya bi don karar da 'yan ta'adda

- Ministan tsaro na Najeriya ya kirayi gwamnoni da su koma su magance rashin tsaro jioinsu

- Ya bayyana cewa, ba akkin gwamnatin tarayya kadai bane magance rasin tsaron a Najeriya

- Ya ce kuka da cewa gwamnatin tarayya ta dauki matakai bazai haifar da mai ido ba

Gwamnatin tarayya ta bukaci gwamnonin Jihohi da sauran wakilai da su ba da tasu gudummawar wajen magance ‘yan fashi da sauran matsalolin tsaro da ke addabar al’ummar kasar, Daily Trust ta ruwaito.

Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (Rtd) ya ba da wannan furucin a ranar Asabar a Kano bayan ya sake jaddada rajistarsa na jam’iyyar APC a shiyyarsa ta Galadanchi da ke ƙaramar hukumar Gwale ta Jihar Kano.

Da yake amsa tambaya kan matsayar da gwamnatin tarayya ke da ita a kan 'yan ta'adda yayin musayar ra'ayi tsakanin wasu gwamnoni, Ministan ya ce gwamnatin tarayya na nan kan bakanta na kare rayuka da dukiyoyi.

KU KARANTA: 'Yan majalisu na duba kudirin dakatar da 'yan jaridun da basu da digiri daga aiki

FG ga gwamnoni: Akwai hanyoyi da yawa da zaku iya bi don karar da 'yan ta'adda
FG ga gwamnoni: Akwai hanyoyi da yawa da zaku iya bi don karar da 'yan ta'adda Hoto: FRCN
Source: UGC

“Ba za mu iya zama mu ba mutane damar yin magana yadda suke so ba. Ya kamata suyiwa mutanensu aikin da wajaba akansu. Ya kamata duka gwamnoni suyi aikin kansu. Suna da abubuwa da yawa da zasu iya yi don dakatar da wannan ta'addancin da sauran al'amuran tsaro.

“Amma kukan cewa ya kamata mu aikata hakan ko kuma kada mu aikata hakan ba zai magance matsalar ba.

"Kowa ya koma wurin mutanensa. Kowa, ina nufin, duk masu rike da mukaman siyasa su koma yankunansu su ga abin da ke faruwa a can. Akwai talauci, akwai sakaci, babu makaranta, babu cibiyoyin kiwon lafiya, babu komai!

"Don haka, idan za su iya mai da hankali kan hakan shi kadai, ina ganin kasar za ta kubuta," in ji shi.

KU KARANTA: NDLEA ta bankado gidan ajiyar tabar wiwi, ta kama mota makare da kwayoyi a Benue

A wani labarin, Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya shawarci ‘yan siyasan Najeriya da kada su dauki zabe a matsayin juyin mulki ko yaki, a’a su hadu su goyi bayan duk wanda ya samu nasara, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake magana a Yenegoa, babban birnin jihar Bayelsa yayin bikin nuna godiya / bikin cika shekara daya da Gwamna Douye Diri na mulki, Jonathan ya kuma shawarci wadanda ke cikin siyasa da kada su yi riko da dacin rai.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel