'Yan majalisu na duba kudirin dakatar da 'yan jaridun da basu da digiri daga aiki
- Majalisar wakilai na kasa na duba yiwuwar dakatar da 'yan jaridun da basu da digiri
- Hakan wani yunkuri ne na inganta yada labarai a kasar ta Najeriya in ji majalisar
- Majalisar ta kuma bayyana yadda dokar za ta kasance domin ganin ta tafi yadda ya dace
Majalisar Wakilai na aiki kan wani kudiri da ke neman daukaka cancantar aikin jarida a Najeriya, wanda hakan ya zama tilas ga masu aikin jarida su nemi digiri ko difloma kan kwasa-kwasan da suka shafi aikin jarida.
Shawarwarin na kunshe ne a cikin Dokar Kwaskwarimar Yarjejeniyar 'Yan Jaridun Najeriya ta 2019 wacce Mista Francis Agbo ya dauki nauyi, wacce aka tsara karantarta a zama na biyu.
Kudirin, wanda wakilin jaridar Punch ya samu kwafinsa, musamman yana neman gyara Sashe na 19 (1) (a), 19 (1) (b), 21 (5) (a), 21 (5) (b) da 35 na Dokar Majalisar 'Yan Jaridu ta Najeriya Dokar N128 LFN 2004.
KU KARANTA: Da Trump ya gayyaci Ganduje, da ya koya masa yadda ake cin zabe, Doguwa
Lokacin da aka yi kwaskwarima, sabuwar dokar za ta samar da cewa:
"mutum da ke da digiri na farko, Babban difloma na kasa a aikin Jarida, Fasahar Watsa Labarai ko Sadarwa, ko kuma takardar shaidar kammala karatun digiri na biyu zai yi aikin dan jarida."
Hakanan zai kara hukunci da tara ga 'yan jaridar da basu da horo da kuma na jabu.
Za a share sakin layi na (a) na Sashe na 19 (1) kuma a maye gurbinsa da sabo wanda ya karanta:
“19 (1) (a) yana da digiri na farko, takardar shaidar difloma ta kasa ko kuma kwatankwacinsa a aikin Jarida, Fasahar Bayanai ko Sadarwa daga kowace babbar makranta a Najeriya ko wani wuri. ”
“19 (1) (b) a game da mutumin da ke da digiri na farko a kowane fanni, zai kasance a cikin shekaru biyar ya sami takardar shaidar kammala karatun aikin jarida, watsa labarai, sadarwa ko wani fannin da ya shafi hakan daga wata babbar jami’a a Najeriya ko wani wuri."
KU KARANTA: Gobara ta cinye shaguna kusan 100 daura da kasuwar Wunti da ke Bauchi
A wani labarin, Matsalar tsaro a Najeriya ta dauki wani sabon salo a ranar Laraba tare da kashe-kashe da satar mutane a fadin jihohin kasar, The Nation ta ruwaito.
A Abuja, ‘yan majalisar tarayya sun fara gabatar da zaman su na 2020 tare da muhawara kan rashin tsaro a Majalisar Dattawa da wani jawabi mai karfi da Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya yi, wanda ya shafi rashin tsaro.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng