Bai kamata 'yan siyasa suke ganin zabe a matsayin juyin mulki ba, in ji Jonathan

Bai kamata 'yan siyasa suke ganin zabe a matsayin juyin mulki ba, in ji Jonathan

- Tsohon shugaban kasar Naajeriya ya shawarci 'yan siyasa da suk daina daukar siyasa da gaba

- Goodluck Jonathan ya ce siyasa bai kamata ta kasance kamar juyin mulki ba, demokradiyya ce

- Ya kuma ja hankalin masu mulki da su dauki nauyin kowa a inda suke mulki ba iya wadanda suka zabe su ba

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya shawarci ‘yan siyasan Najeriya da kada su dauki zabe a matsayin juyin mulki ko yaki, a’a su hadu su goyi bayan duk wanda ya samu nasara, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake magana a Yenegoa, babban birnin jihar Bayelsa yayin bikin nuna godiya / bikin cika shekara daya da Gwamna Douye Diri na mulki, Jonathan ya kuma shawarci wadanda ke cikin siyasa da kada su yi riko da dacin rai.

KU KARANTA: NDLEA ta bankado gidan ajiyar tabar wiwi, ta kama mota makare da kwayoyi a Benue

Bai kamata 'yan siyasa suke ganin zabe a matsayin juyin mulki ba, in ji Jonathan
Bai kamata 'yan siyasa suke ganin zabe a matsayin juyin mulki ba, in ji Jonathan Hoto: PRI.org
Source: UGC

Ya ce, “Tsarinmu na dimokiradiyya doka ta amince da shi, don haka bai kamata 'yan siyasa na zamani su fara aiwatar da dimokiradiyya da neman mulki kamar muna shirya juyin mulki ba.

“A karshen tsarin siyasa, muna sa ran cewa bangarorin biyu su hadu wuri daya kuma wanda ya ci nasara yana dauke da nauyin kowa.

"Shugabannin da suka fafata a zabe dole ne su san cewa tsari ne na siyasa wanda doka ta sani, kuma duk wanda ya yi nasara, mun yarda cewa Allah ne Ya ba shi wannan matsayin.

“Ina son na gode wa Gwamna Diri saboda bude hannuwansa da kuma maraba da duk wani dan jihar Bayelsa, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba. A lokacin da ka ci zabe a lokacin ka zama gwamnan kowa,” in ji shi.

KU KARANTA: Ban yi imani da bayyana soyayya a fili ba, na fi son ta sirri, in ji Rahama Sadau

Shima da yake magana, Gwamna Diri yayi godiya ga Allah wanda ya bashi damar yiwa jihar aiki a wannan matsayin, duk da kuwa akwai lokacin da bai tsammaci hakan ba.

Ya ce nasarar da ya samu a Kotun Koli a ranar 13 ga Fabrairu, 2020 amsa ce ta addu'o'in bayin Allah da kuma mutanen jihar.

A wani labarin, Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Doguwa, ya ce tsohon shugaban Amurka Donald Trump ba zai iya faduwa zabe ba idan da ya nemi taimakon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

Mista Doguwa, wanda ke wakiltar Mazabar Tudunwada/Doguwa, ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da aka turowa jaridar Daily Nigerian a ranar Laraba, yayin da yake yiwa magoya bayansa jawabi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel