NDLEA ta bankado gidan ajiyar tabar wiwi, ta kama mota makare da kwayoyi a Benue

NDLEA ta bankado gidan ajiyar tabar wiwi, ta kama mota makare da kwayoyi a Benue

- Hukumar NDLEA ta sake samu nasarar cafke wasu bata-gari a wani yankin jihar Benue

- Hukumar ta kame wata mota makare da tabar wiwi a kan hanyar ta zuwa jihar Nasarawa

- Hakazalika ta bankado wani dakin ajiyar tabar ta wiwi a wani yankin na jihar Benue

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), ta gano wata ma'ajiya ta tabar wiwi a yankin karamar hukumar Guma ta jihar Benue, Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun hukumar, Jonah Achema, ya fadi haka a ranar Asabar a Abuja cewa hukumar ta kuma kama wata babbar motar daukar muggan kwayoyi a jihar.

Da take bayar da bayani game da miyagun kwayoyi da aka kama a Benue, ga Shugaban Hukumar, Brig-Gen. Mohamed Buba Marwa, kwamandan hukumar ta NDLEA, Misis Florence Ezeonye, ​​ta ce adadin buhunan wiwi da aka kama a yayin kamen ya kai kilogram 1,578.

KU KARANTA: Ban yi imani da bayyana soyayya a fili ba, na fi son ta sirri, in ji Rahama Sadau

NDLEA ta bankado gidan ajiyar tabar wiwi, ta kama mota makare da kwayoyi a Benue
NDLEA ta bankado gidan ajiyar tabar wiwi, ta kama mota makare da kwayoyi a Benue Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

A cewar ta: “Jami’an hukumar ta NDLEA reshen jihar Benue a cikin Makurdi, ta cake wata tirela da bata dauke da komai daga Awka, jihar Anambra da ke kan hanyarta ta zuwa Lafia, jihar Nasarawa.

"Amma lokacin da aka bincika ta yadda ya kamata, an gano bulo 600 na tabar wiwi mai nauyin 600kg a wani daki da aka gina a karkashin motar.” in ji Ezeonye.

A cewar ta, yanayin ɓoyewar shine irin sa na farko.

Ta kara da cewa: “An sake yin kamun ne yayin da mutanenmu suka afka wa wani sito cike da kwayoyi da wasu manoma suka girba a yankin karamar hukumar Guma da karfe 3 na safe.

“Adadin haramtattun magunguna da aka kwashe daga dakin ajiyar ya kai kilogram 978.

"Dillalan miyagun kwayoyi sun harbe mutane na yayin da suka gansu amma an dakile harin nasu kuma a saboda haka, ba mu samu wani rauni ba."

KU KARANTA: Gobara ta cinye shaguna kusan 100 daura da kasar Wunti da ke Bauchi

A wani labarin, Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce ta gano wani kauyen da ake nomar wiwi a karamar hukumar Owan West ta jihar Edo, The Cable ta ruwaito.

Buba Wakawa, kwamandan NDLEA a Edo, ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Benin, babban birnin jihar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.