Ban yi imani da bayyana soyayya a fili ba, na fi son ta sirri, in ji Rahama Sadau

Ban yi imani da bayyana soyayya a fili ba, na fi son ta sirri, in ji Rahama Sadau

- Shahararriyar tauraruwar masa'antar fina-finai na Kannywood ta bayyana ra'ayinta kan soyayya

- A cewar ta soyayya abu ne na sirri da ya kamata da boye kada duniya ta sani sai ita kadai

- Ta bayyana cewa, ita soyayya ta fi son ya zama na daga ita sai wadda ta ke so shikenan

Tauraruwar Kannywood, Rahama Sadau ta ce ba ta yi imani da bayyana soyayya da babbar murya ba kamar yadda ta fi so ta sanya rayuwar soyayyar ta zama sirri, Daily Trust ta ruwaito.

Ta bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ta yada a shafinta na Twitter, @Rahma_sadau ranar Juma'a.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa ta gayyaci Gwamnan CBN yayi bayani kan haramta Bitcoin

Ban yi imani da bayyana soyayya a fili ba, na fi son ta sirri, in ji Rahama Sadau
Ban yi imani da bayyana soyayya a fili ba, na fi son ta sirri, in ji Rahama Sadau Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

“To dai, na fi son kiyaye shi shirri. Abu daya ne duniya ta san ku hakanan wani abu ne daban na "shi" (shi kadai) ya san kuma ya riski gaskiyar ki," kamar yadda ta wallafa.

Sadau, wacce ta yi suna a karshen shekarar 2013 bayan ta shiga masana’antar finafinai ta Kannywood tare da fim dinta na farko Gani ga Wane, ta kara da cewa “Ban yi imani da soyayya a bayyane da babbar murya ba. Ina son sirri na.”

KU KARANTA: Da Trump ya gayyaci Ganduje, da ya koya masa yadda ake cin zabe, Doguwa

A wani labarin, Wata matar mai suna Ramatu Idris da ke Unguwar Malam Lamu, Tankarau, Unguwar Dutsen Abba da ke karamar Hukumar Zariya, ta bayyana yadda ’yan fashi suka sanya ta zama bazawara bayan wata daya da aurenta da marigayi Yusuf Suleiman.

Idris ya fadawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Alhamis cewa lamarin ya faru ne a ranar 4 ga Fabrairu, da misalin karfe 12:45 na rana, kwanaki 28 bayan aurenta da Suleiman, The Nation ta ruwaito.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel