Da Trump ya gayyaci Ganduje, da ya koya masa yadda ake cin zabe, Doguwa

Da Trump ya gayyaci Ganduje, da ya koya masa yadda ake cin zabe, Doguwa

- Wani dan majalisa ya bayyana dalilai a mahangarsa dangane da faduwar Donald Trump

- Alhassan Doguwa, ya bayyana cewa, Ganduje wata cibiyar siyasace da babu irinta a Najeriya

- Yace, da Donald Trump ya nemi shawarin Ganduje da ba yadda za a yi ya fadi a zaben Amurka

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Doguwa, ya ce tsohon shugaban Amurka Donald Trump ba zai iya faduwa zabe ba idan da ya nemi taimakon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

Mista Doguwa, wanda ke wakiltar Mazabar Tudunwada/Doguwa, ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da aka turowa jaridar Daily Nigerian a ranar Laraba, yayin da yake yiwa magoya bayansa jawabi.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: WTO za ta nada Darakta-Janar a ranar Litinin mai zuwa

Da Trump ya gayyaci Ganduje, da ya koya masa yadda ake cin zabe, Doguwa
Da Trump ya gayyaci Ganduje, da ya koya masa yadda ake cin zabe, Doguwa Hoto: This Day
Asali: UGC

“Idan aka duba, lokacin da alkaluman suka fara nuna Trump zai sha kaye, ya kamata ya kira Ganduje a waya ya tura masa Murtala Garo ko Alhassan Ado ko Kawu Sumaila ko dan majalisa Kabiru Rurum. Labarin ba zai kasance haka ba a yau.

“A wurinmu, Ganduje cibiya ce ta siyasa. 'Yan siyasa za su kwashe shekaru suna gaya muku karya game da cin zabe a 2023, kawai suna gaya muku shirme ne," in ji Mista Doguwa a cikin gajeren faifan.

Yawancin masu sa-ido masu zaman kansu suna da ra'ayin cewa jam'iyyar APC mai mulki tare da hadin gwiwar jami'an tsaro da manyan jami'an Hukumar Zabe ta Kasa mai zaman kanta, (INEC), sun yi magudi a zaben da aka yi a Maris 2019 don goyon bayan jam'iyya mai mulki.

KU KARANTA: Ya kamata Buhari ya dama da Inyamurai a nadin hafsoshi, in ji Yarbawa

A wani labarin, Akalla likitocin mata 47 'yan jihar Kano sun dawo daga Sudan bayan sun kammala karatunsu cikin nasara wanda gwamnatin jihar ta dauki nauyi, Premium Times ta ruwaito.

Abba Anwar, babban sakataren labarai na gwamnan, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar a Kano.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.