Abun dariya: Sai da jami’ai suka zage suka tura ta, motar da kwaso masu zanga-zanga da aka kama ta tsaya cak

Abun dariya: Sai da jami’ai suka zage suka tura ta, motar da kwaso masu zanga-zanga da aka kama ta tsaya cak

- Wata motar yan sanda da aka yi amfani da ita wajen kwasar masu zanga-zangar #OccupyLekkiTollGate da aka kama a ranar Asabar, 13 ga watan Fabrairu, ta tsaya cak

- Sai da jami’an kamfanin LCC suka tura motar inda aka mayar da masu zanga-zangar zuwa wata mota daban

- Lamarin ya haddasa zazzafan martani daga yan Najeriya a shafin soshiyal midiya

Yayinda ake tsaka da fargaba sakamakon kama masu zanga-zangar #OccupyLekkiTollGate da aka yi a ranar Asabar, 13 ga watan Fabrairu, an dan samu nutsuwa na dan lokaci bayan motar yan sandan ya tsaya cak.

Motar yan sandan wanda a kan yi amfani da shi wajen daukar fursunoni, shine aka yi amfani da shi waen kama masu zanga-zangar, Channels TV ta ruwaito.

A cewar kafar watsa labaran, sai da jami’an kamfanin Lekki Concession Company (LCC) suka tura motar.

Abun dariya: Sai da jami’ai suka zage suka tura ta, motar da kwaso masu zanga-zanga da aka kama ta tsaya cak
Abun dariya: Sai da jami’ai suka zage suka tura ta, motar da kwaso masu zanga-zanga da aka kama ta tsaya cak Hoto: @Osas_BigEngine, @ManUtdInPidgin
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada wani sabon shugaban tsaro

Legit.ng ta tattaro cewa an mayar da masu zanga-zangar da aka kama ne zuwa wata mota daban.

Yan Najeriya sun yi martani

Lamarin ya janyo martani daga yan Najeriya a shafin soshiyal midiya. Legit.ng ta tattaro wasu daga cikinsu a kasa:

Stone, @ stonekay2000, ya ce a Twitter:

"Rashin kwarewa a komai. Gwamnatin Najeriya da wakilansu na zalunci."

Toydad_official, @toydadofficial, ya ce:

"Kasa da ta gaza a kulla yaumin komai baya tafiya daidai ba a Najeriya"

tiMTimI, @Magnus3001, ya ce:

"Wannan shi ne yadda hukumomin dokarmu suka shirya: hatta motar 'yan sanda ma na zanga-zangar, sama da' yan sanda 100 a harabar tollgate. Toh Wanene ke zanga-zanga kenan?"

KU KARANTA KUMA: FG ta ce ma’aikatan jami’a sun yarda da janye yajin aiki, ta yi karin haske kan bude jami’o’i a fadin kasar

A baya mun kawo cewa ana zaman dar-dar a Legas a ranar Asabar, 13 ga Fabrairu, yayin da ‘yan sanda a jihar suka kama wasu masu zanga-zangar #OccupyLekkiTollGate.

Masu zanga-zangar sun mamaye harabar tollgate ne domin yin gangamin kin amincewa da karbo wajen da kamfanin Lekki Concession Company (LCC)tayi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ku tuna cewa tollgate ta zamo kara zube ba tare da masu kula da ita ba tun lokacin da lamarin harbi tsakanin rundunar sojin Najeriya da masu zanga-zangar ya wakana a ranar 20 ga watan Oktoba 2020.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel