FG ta ce ma’aikatan jami’a sun yarda da janye yajin aiki, ta yi karin haske kan bude jami’o’i a fadin kasar

FG ta ce ma’aikatan jami’a sun yarda da janye yajin aiki, ta yi karin haske kan bude jami’o’i a fadin kasar

- Gwamnatin tarayya ta ci gaba da tattaunawa da ma’aikatan jami’ar da ke yajin aiki

- Ma’aikatar kwadago na da kwarin gwiwar cewa za a warware takaddamar da ke tsakaninsu da kungiyoyin

- Ma’aikatan da ke yajin aiki na korafi ne kan tsarin da gwamnatin tarayya ta dauka wajen biyan mambobinta albashi

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa harkokin karatu a jami’o’in gwamnati za su ci gaba nan ba da jimawa ba bayan yarjejeniyar da ta cimma tare da ma’aikatan jami’ar da ke yajin aiki.

A cewar jaridar The Nation, ma'aikatar kwadago da daukar ma’aikata ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, 12 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama masu zanga-zanga da dama a Lekki tollgate

FG ta ce ma’aikatan jami’a sun yarda da janye yajin aiki, ta yi karin haske kan bude jami’o’i a fadin kasar
FG ta ce ma’aikatan jami’a sun yarda da janye yajin aiki, ta yi karin haske kan bude jami’o’i a fadin kasar Hoto: @LabourMinNG
Source: Twitter

Gwamnatin ta yi bayanin cewa ta cimma yarjejeniya tare da shugabannin kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya da na ma’aikatan jami’o’i(NASU), da nufin kawo karshen yajin aikin a ranar 15 ga Fabrairu.

Mahukuntan sun ce rahotannin kafafen yada labarai wanda ke ikirarin cewa ganawar da aka yi tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadagon a ranar 11 ga watan Fabrairu ba ta haifar da ‘da mai idanu ba, ba gaskiya bane.

Sanarwar ta karanto cewa:

“Ganawar ba ta ƙare a rashin dadin rai ba. Maimakon haka, an cimma yarjejeniya kan wasu batutuwa kuma an rubuta su a matsayin Yarjejeniyar fahimta sannan aka ba shugabannin kungiyoyin kwadagon biyu su je su tuntubi mutanensu da nufin dakatar da yajin aikin zuwa ranar Litinin, 15 ga Fabrairu, 2021.”

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa kungiyoyin kwadagon sun fara yajin aiki ne a kan yadda gwamnati ke tafiyar da tsarin biyan albashin ma’aikata na bai daya (IPPIS) da sauran batutuwa.

A wani labarin, an kara albashin ma’aikatan gwamnati a jihohin Ribas da Imo bisa daidai da tsarin biyan karancin albashi na N30,000.

KU KARANTA KUMA: Disamba 2020: Kason da kowani bangare ya kwashe daga N601.11bn na kudaden da FG ke rabawa duk wata

Gwamna Nyesom Wike na Ribas da takwaransa na Imo, Hope Uzodinma, sun sanar da cewa daga yanzu ma’aikata a jihohin su za su ci moriyar sabon mafi karancin albashin tare da gyara a albashin kowa kamar yadda gwamnatin tarayya ta amince.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Ribas ta sanar da aiwatar da manufar a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 11 ga watan Fabrairu, ta hannun kwamishinan yada labarai da sadarwa, Paulinus Nsirim.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel