Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama masu zanga-zanga da dama a Lekki tollgate
- Zanga-zangar #OccupyLekkiTollGate da aka shirya a jihas Lagas ya hadu da cikas daga rundunar yan sanda
- Masu zanga-zangar sun shirya gudanar da gangami na adawa da sake bude Lekki tollgate, wurin da ake zargin an yi harbe-harbe a ranar 20 ga Oktoba, 2020
- Sai dai kuma, an tattaro cewa hukumar tsaron ta kama masu zanga-zanga fiye da 10 a wajen
Ana zaman dar-dar a Legas a ranar Asabar, 13 ga Fabrairu, yayin da ‘yan sanda a jihar suka kama wasu masu zanga-zangar #OccupyLekkiTollGate.
Masu zanga-zangar sun mamaye harabar tollgate ne domin yin gangamin kin amincewa da karbo wajen da kamfanin Lekki Concession Company (LCC)tayi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ku tuna cewa tollgate ta zamo kara zube ba tare da masu kula da ita ba tun lokacin da lamarin harbi tsakanin rundunar sojin Najeriya da masu zanga-zangar ya wakana a ranar 20 ga watan Oktoba 2020.
Sai dai kuma, a kwanan ne Kwamitin bincike na shari'a kan rikicin #EndSARS ya amince da bukatar kamfanin LCC na karbar ragamar kula da wurin.
KU KARANTA KUMA: Disamba 2020: Kason da kowani bangare ya kwashe daga N601.11bn na kudaden da FG ke rabawa duk wata
Wannan ci gaban ya fusata masu zanga-zangar #EndSARS lamarin da ya haifar da wani zagaye na zanga-zangar da aka yiwa lakabi da #OccupyLekkiTollGate.
‘Yan sanda sun lashi takobin yin maganin masu zanga-zangar
Biyo bayan shawarar da masu zanga-zangar suka yanke, ‘yan sandan Legas sun ce ba za su bari a yi wata zanga-zangar da za ta sake haifar da lalata kadarori da dukiyoyin gwamnati ba.
Hakeem Odumosun, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas, ya yi wannan gargadin yayin ganawa da manema labarai a Ikeja a ranar Alhamis, 11 ga watan Fabrairu.
A baya mun ji cewa 'Yan sandan jihar Legas sun tsaya tsayin daka wurin dakatar da zanga-zangar End SARS wacce matasa suka shirya farawa a ranar Asabar a Lekki toll gate.
Runduna ta musamman ta 'yan sandan jihar Legas ne suka tabbatar da dakatarwar, The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Babbar magana: An kama ango yana tarawa da kawar amarya a ranar daurin aurensu
"CSP Yinka Egbeyemi wanda yanzu haka ya jagoranci 'yan sanda domin tsaron Lekki Toll Gate (Admiralty Plaza) Obalende, Ikoyi, Jakande Roundabout, da wasu bangarori na Eti Osa," kamar yadda RRS suka wallafa a shafinsa na Twitter ranar Juma'a da daddare.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng