Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada wani sabon shugaban tsaro

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada wani sabon shugaban tsaro

- Gwamnatin Najeriya ta sanar da sauya shugabanci a hukumar DIA

- Sabon nadin ya biyo bayan ritayar da tsoffin shugabannin tsaro suka yi

- Tuni Manjo-Janar Samuel Adebayo tuni ya fara sabon aikinsa a hukumar DIA

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo-Janar Samuel Adebayo a matsayin sabon babban hafsan leken asirin tsaro na Najeriya (CDI) kuma shugaban hukumar leken asirin tsaro na kasa(DIA).

Gwamnatin Najeriya ta sanar da nadin sabon kwamandan tsaron a shafinta na Twitter a ranar Asabar, 13 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin Nigeria 2 sun kara albashin ma’aikata duk da matsin tattalin arziki

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada wani sabon shugaban tsaro
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada wani sabon shugaban tsaro Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Manjo-Janar Samuel Adebayo ya gaji Air Vice Marshal Muhammed Usman, wanda ya yi ritaya daga aikikwanan nan.

Sanarwar ta ce: “Shugaba @ MBuhari ya nada Maj.-Gen. Samuel Adebayo a matsayin sabon babban hafsan leken asirin tsaro na Najeriya (CDI) kuma shugaban hukumar leken asirin tsaro (DIA). Ya maye gurbin Air Vice Marshal Muhammed Usman, wanda ya yi ritaya daga aiki kwanan nan.”

KU KARANTA KUMA: FG ta ce ma’aikatan jami’a sun yarda da janye yajin aiki, ta yi karin haske kan bude jami’o’i a fadin kasar

A gefe guda, majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta bai wa sabbin hafsoshin soji da ya nada wa'adin kawo karshen matsalar tsaro, garkuwar da mutane, 'yan bindiga da sauran kalubalen tsaron da suka addabi kasar nan.

A yayin zantawa da manema labarai a Abuja a jiya, shugaban kwamitin majalisar a kan harkokin sojoji, Sanata Ali Ndume, ya ce idan Buhari ya samar da abubuwan bukata ga sabbin hafsoshin tsaro, ya basu wa'adi a kan aikin da yake so su yi.

Kamar yadda yace, kada gwamnati ta bata lokaci wurin maye gurbinsu da wasu idan suka gaza, Vanguard ta wallafa.

A wani labarin, mun ji a baya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura sunayen tsofaffin hafsoshin tsaro, inda ya bukaci a tantance su domin a ba su mukamai.

Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin yada labarai ta kafafen zamani, Bashir Ahmaad, ya bada wannan sanarwa a shafinsa na Twitter.

Bashir Ahmaad ya bayyana cewa shugaban kasa ya aika takarda zuwa ga shugaban majalisa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan game da batun.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng