Gobara ta cinye shaguna kusan 100 daura da kasuwar Wunti da ke Bauchi

Gobara ta cinye shaguna kusan 100 daura da kasuwar Wunti da ke Bauchi

- Wata gobara ta tashi cikin dare a kasuwar jihar Bauchi ta kuma cinye dukiyoyi da yawa

- Hukumar kashe gobara ta samu nasarar hana yaduwar gobarar zuwa wani yankin kasuwar

- Gwamnan jihar ya halarci wajen yayin da ya jajantawa wadanda abin ya shafa da safiya

Dukiyoyi na miliyoyin nairori sun lalace a gobarar tsakar daren jiya wanda ya lalata ɗayan manyan rukunin shagunan sayayya a cikin garin Bauchi mai suna Bababa Shopping Complex wanda ke kusa da kasuwar Wunti, NigerianTribune ta ruwaito.

Bayanai da aka tattara sun bayyana cewa gobarar ta fara ne a daren Juma'a kuma ta tashi har zuwa wayewar garin Asabar yayin da jami'an kashe gobara daga Hukumar kashe gobara ta jihar, ATAP, ATBU da FedPoly suka yi kokarin shawo kan wutar daga yaduwa.

Rukunin shagunan wanda yake da aƙalla shaguna 100 da rumfuna sun ƙone kurmus ba tare da an cire komai ba kasancewar masu shagunan sun rufe shagunansu kuma sun tafi gida.

KU KARANTA: Da Trump ya gayyaci Ganduje, da ya koya masa yadda ake cin zabe, Doguwa

Wuta ta cinye wasu shaguna a kusa da kasar Wunti da ke Bauchi
Wuta ta cinye wasu shaguna a kusa da kasar Wunti da ke Bauchi Hoto: Information Nigeria
Asali: UGC

Duk da cewa babu wanda ya iya gano musabbabin tashin gobarar saboda wutar ta tashi ne lokacin da aka dawo da wutar lantarki da ta haifar da tartsatsin wuta daga wasu shagunan da aka bar wuta a kunne.

Gwamnan jihar Bauchi, Sen Bala Mohammed Abdulkadir ya hadu da wasu a wurin da gobarar ta tashi cikin dare da zaran jin labarin. An ganshi yana shiga cikin aikin ceton.

Gwamnan ya jajantawa wa wadanda lamarin ya rutsa da su inda ya bukace su da su dauki hakan a matsayin kaddara, yana mai godewa Allah cewa ba a rasa rai ba a wannan bala'in duk da cewa dukiya ta salwanta.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa ta gayyaci Gwamnan CBN yayi bayani kan haramta Bitcoin

Bala Mohammed wanda ya kasance a wurin na 'yan awanni ya tabbatar da cewa hukumomin da abin ya shafa zasu yi binciken musabbabin gobarar.

Hakazalika ya kuma yi alkawarin cewa gwamnati za ta hanzarta daukar matakan taimaka wa wadanda lamarin ya shafa ta hanyar rage musu asarar.

A wani labarin, Wata matar mai suna Ramatu Idris da ke Unguwar Malam Lamu, Tankarau, Unguwar Dutsen Abba da ke karamar Hukumar Zariya, ta bayyana yadda ’yan fashi suka sanya ta zama bazawara bayan wata daya da aurenta da marigayi Yusuf Suleiman.

Idris ya fadawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Alhamis cewa lamarin ya faru ne a ranar 4 ga Fabrairu, da misalin karfe 12:45 na rana, kwanaki 28 bayan aurenta da Suleiman, The Nation ta ruwaito.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel