NDLEA ta bankado wani kauyen wiwi, ta cafke kwayoyi ‘masu darajar N1.4bn’ a Edo

NDLEA ta bankado wani kauyen wiwi, ta cafke kwayoyi ‘masu darajar N1.4bn’ a Edo

- Rundunar NDLEA a jihar Edo ta samu nasarar kame wasu bata-gari da laifin noman tabar wiwi

- Rundunar ta kame mutane bakwai tare da kwace bindigogi biyu a wani babban rumbun adana kaya

- An kiyasta adadin kudin tabar wiwi din da aka kame zai haura kudi N1.4bn bayan wanda aka lalata

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce ta gano wani kauyen da ake nomar wiwi a karamar hukumar Owan West ta jihar Edo, The Cable ta ruwaito.

Buba Wakawa, kwamandan NDLEA a Edo, ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Benin, babban birnin jihar.

Ya ce rundunar ta cafke wasu mutane bakwai wadanda ke boye wiwi a manyan rumbunan adana kaya guda hudu a dajin Ukpuje da ke Owan West.

Wakawa ya ce, rumbunan ajiyar guda hudu suna makare da buhu 16, 344 na tabar wiwi, masu nauyin kilogram 233, 778, wadanda aka kame ban da wasu bindigogi biyu.

Kwamandan ya ce an kiyasta kimar kudin miyagun kwayoyin da aka kama a kan N1.4billion.

Ya ce an kama mutane bakwai da ake zargi tare da tsare su a hannun hukumar ta NDLEA. Ya bayyana sunayensu da; Emmanuel Oki, mai shekara 62, wanda shi ne shugaban kungiyar masu kwayoyin Ukpuje.

Sauran su ne Gowon Ehimigbai mai shekara 53; Enodi Ode mai shekara 37; Ayo Oni mai shekara 30, Akhime Benjamin mai shekara 43, ; Odi Sabato mai shekara 42, da Bright Inemi Edegbe mai shekara 53.

KU KARANTA: Buhari zai kaddamar da aikin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi ranar Talata

NDLEA ta bankado wani kauyen wiwi, ta cafke kwayoyi ‘masu darajar N1.4bn’ a Edo
NDLEA ta bankado wani kauyen wiwi, ta cafke kwayoyi ‘masu darajar N1.4bn’ a Edo Hoto: The Cable
Asali: UGC

A cewar Wakawa, kamun shi ne mafi yawan tarin wiwi da rundunar ta gano.

Ya bayar da bayanin adadin kamar haka: buhu 318 na kilogram 80 kowannensu mai nauyin 25,440kg; Buhu 15,853 na kilogram 13 masu nauyin kilogram 206,089.

Hakazalika, jimillar adadin da aka kama ya kai kilogram 2,249, wasu kuma masu nauyin kilogram 231,529 an lalata su a cikin rumbunan.

Kwamandan ya danganta nasarar da aka samu a aikin bisa goyon bayan Buba Marwa, shugaban NDLEA.

“Mun dauki sabbin motoci kirar Hilux guda biyu da aka kaddamar ga rundunar a makon da ya gabata.

"Wannan shine aikin farko na motocin kuma ya zama mafi gwabi ga rundunar. Muna godiya ga shugaban, kuma wannan gargadi ne karara cewa babu sararin fataucin miyagun kwayoyi a jihar.” inji shi.

NDLEA ta bankado wani kauyen wiwi, ta cafke kwayoyi ‘masu darajar N1.4bn’ a Edo
NDLEA ta bankado wani kauyen wiwi, ta cafke kwayoyi ‘masu darajar N1.4bn’ a Edo Hoto: The Cable
Asali: UGC

Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, Marwa ya ce gwamnatinsa za ta fitar da dillalan kwayoyi daga maboyarsu.

KU KARANTA: Baya ga Najeriya, akwai kasashe bakwai da suka haramta cinikin Bitcoin

A wani labarin, Jami'an hadin gwiwa na ma'aikatar Albarkatun Kasa ta jihar Ondo sun kama mutane hudu da laifin noman tabar wiwi a cikin dajin Akure, The Nation ta ruwaito.

An kama su ne saboda lalata bishiyoyin tattalin arziki da nufin dasa itacen tabar wiwi. Daraktan rundunar hadin gwiwa a ma’aikatar, Alhaji Moshood Obadun, ya ce an cafke wadanda ake zargin ne bayan da suka yi bayani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel