Olonisakin, Buratai, Ibok-Ete Ibas da Siddique za su zama Jakadu a kasashen waje
- Muhammadu Buhari ya kara sunayen wadanda zai nada Jakadu a kasar waje
- Shugaban kasar ya aikawa Majalisa sunan tsofaffin hafsun sojojin da ya cire
- Hakan na zuwa mako guda bayan ya sauke shugabannin tsaro, ya nada wasu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura sunayen tsofaffin hafsoshin tsaro, inda ya bukaci a tantance su domin a ba su mukamai.
Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin yada labarai ta kafafen zamani, Bashir Ahmaad, ya bada wannan sanarwa a shafinsa na Twitter.
Bashir Ahmaad ya bayyana cewa shugaban kasa ya aika takarda zuwa ga shugaban majalisa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan game da batun.
Mai girma Muhammadu Buhari ya na so tsofaffin shugabannin tsaro na kasar da ya sauke, su rike kujerar Jakadun Najeriya a kasashen ketare.
KU KARANTA: Buratai ya bar gidan soja bayan shekara 40 a bariki
Shugaba Muhammadu Buhari ya dogara ne da sashe nan a 171 (1), (2) (c) da karamin sashe na (4) na kundin tsarin mulki wajen bada mukaman.
Kamar yadda hadimin shugaban kasar ya bayyana dazu nan, an aika sunayen mutane biyar ne zuwa ga majalisar dattawan a yau ranar Alhamis.
Ga sunayen kamar haka: Janar Abayomi G. Olonisakin (Rtd), Laftana Janar Tukur Y. Buratai (Rtd), da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (Rtd).
Haka zalika Air Marshal Sadique Abubakar (Rtd), da Air Vice Marshal Mohammed S. Usman (Rtd) sun shiga cikin wannan jeri da aka fitar.
KU KARANTA: Lauya ya nemi a tursasawa Buhari ya nada sabon Sufetan ‘Yan Sanda
Shugaban kasar ya nemi ‘yan majalisar dattawa su yi la’akari da bukatar da ya gabatar, su amince da nadin da ya ke neman yi na Jakadun Najeriya.
A makon da ya wuce ne Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai, ya mika tutan fara aiki ga sabon shugaban hafsan sojojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahir.
Bayan tsawon shekaru kusan biyar da rabi, an yi sababbin Hafsohin tsaro a Najeriya. Ana sa ran sababbin hafsun tsaron su kawo zaman lafiya.
Air Vice Marshal Mohammed Saliu Usman ya rike mukamin CDI, kafin shugaba Buhari ya cire shi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng