Rashin tsaro: Ka bai wa sabbin hafsoshin tsaro wa'adin kawo canji, Ndume

Rashin tsaro: Ka bai wa sabbin hafsoshin tsaro wa'adin kawo canji, Ndume

- Shugaban kwamitin soji na majalisar dattawa ya bukaci Buhari da ya bai wa sabbin hafsoshin soji wa'adin kawo sauyin tsaro

- Ya bukaci gwamnati da ta fatattakesu tare da maye gurbinsu da wasu matukar suka kasa yin abinda ake so

- Ndume ya yi kira ga sabbin hafsoshin sojin da su fito da tsarin da ya dace wurin yakar rashin tsaro a kasar nan

Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta bai wa sabbin hafsoshin soji da ya nada wa'adin kawo karshen matsalar tsaro, garkuwar da mutane, 'yan bindiga da sauran kalubalen tsaron da suka addabi kasar nan.

A yayin zantawa da manema labarai a Abuja a jiya, shugaban kwamitin majalisar a kan harkokin sojoji, Sanata Ali Ndume, ya ce idan Buhari ya samar da abubuwan bukata ga sabbin hafsoshin tsaro, ya basu wa'adi a kan aikin da yake so su yi.

Kamar yadda yace, kada gwamnati ta bata lokaci wurin maye gurbinsu da wasu idan suka gaza, Vanguard ta wallafa.

KU KARANTA: COVID-19: Ba za mu tirsasawa jama'a yin riga-kafi ba, Sarkin Musulmi

Rashin tsaro: Ka bai wa sabbin hafsoshin tsaro wa'adin kawo sauyi, Majalisar dattawa
Rashin tsaro: Ka bai wa sabbin hafsoshin tsaro wa'adin kawo sauyi, Majalisar dattawa. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Ya ce idan sabbin hafsohin tsaron suka tashi kai rahoto, su tabbatar mai bada shawara kan tsaron kasa ya tsara a kowanne mako.

Ndume ya shawarci sabbin hafsoshin tsaron da su zo da tsarin yaki da ta'addanci wanda a halin yanzu babu shi a kasar nan.

Ya bukaci da a dinga sakin kudi a duk watannin uku ga hukumomin tsaron domin tabbatar da samar da kayan aiki ingantattu garesu.

KU KARANTA: Dan Najeriya ya gina katafaren gida da robobin lemu da ruwa cike da kasa (Hotuna)

A wani labari na daban, NGF ta ce ba canza shugabannin tsaro ne kadai zai kawo garanbawul ba ga matsalolin tsaron da Najeriya take fuskanta, Punch ta wallafa hakan.

Wajibi ne shugaba Muhammadu Buhari ya sanya ido kuma ya dinga bai wa shugabannin tsaro umarni yadda ya dace a matsayinsa na kwamandansu.

"Babban matakin da Buhari zai dauka shine canja salo da kuma fuskantar matsalolin tsaro gadan-gadan. Sai ka ji yana cewa ya taras da tabarbarewar tsaron Najeriya a 2015 ya nunka halin da ake ciki yanzu, wannan kalaman suna matukar tayar da hankali."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel