Kotu ta tsige shugaban PDP da sauran shugabannin jam’iyyar a Ebonyi

Kotu ta tsige shugaban PDP da sauran shugabannin jam’iyyar a Ebonyi

- Har yanzu PDP bata kashe wutar rikicin shugabancinta da ke ruruwa ba a jihar Ebonyi

- Hakan ya kasance ne yayinda kotu ta dakatar da kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar a ranar Laraba

- An kuma rushe kwamitin karkashin jagorancin Fred Udogu yayinda kotu ta bayyana ta a matsayin wacce bata bisa ka’ida

Kotu ta kori Fred Udogu, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ebonyi.

A hukuncin da ta yanke a ranar Laraba, 10 ga watan Fabrairu, wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abaliki, babban birnin jihar, ta kuma bayyana kwamitin PDP karkashin jagorancin Udogu, a matsayin wace bata bisa ka'ida.

Nnachi Okoro, lauyan PDP na bangaren da Onyekachi Nwebonyu ke jagoranta a jihar Ebonyi ya shigar da kara a gaban kotu a watan Nuwamban 2020, yana me neman a rusa bangaren da Udogu ke jagoranta.

Kotu ta tsige shugaban PDP da sauran shugabannin jam’iyyar a Ebonyi
Kotu ta tsige shugaban PDP da sauran shugabannin jam’iyyar a Ebonyi Hoto: @THISDAYLIVE
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojojin Najeriya ta karyata cewar 'yan ta'adda sun kashe sojoji 20 a arewa maso gabas

Mai shigar da karar ya kuma bukaci kotun da ta dawo da shi a matsayin lauyan PDP reshen Ebonyi ba tare da sauraran ta bakin kowani bangare ba.

Yana mai bayyana cire shi da aka yi bayan ficewar Gwamna Dave Umahi a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulki.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Jastis Aluko Akintayo, a cikin hukuncin awanni uku ya yi ikirarin cewa cire Okoro ya saba wa doka sannan ya ba da umarnin a mayar da shi.

Ya kuma umarci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da kar ta amince da kwamitin rikon kwarya da shugabancin PDP na kasa ya kafa a Ebonyi.

Mai Shari'a Akintayo ya kuma yanke hukuncin cewa jam'iyyar PDP ta kasa ta gaza gabatar da hujja gaban kotu game da zargin cin amanar jam’iyya da kokarin rusata da take yi wa shugabancin kwamitin jam'iyyar na jihar Ebonyi.

KU KARANTA KUMA: ‘Yar wasar fim ta ba maza shawarar auren mata rututu domin su daina bin matan banza

A wani labarin, Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce sun tattauna batun sauya sheka da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, daga jam'iyyar PDP ya koma jam'iyyar APC.

A wani bidiyo da aka daura a taron jam'iyyar APC da aka yi a jihar Kogi wanda aka saki a kafar sada zumunta ranar Laraba, Bello ya ce wannan yana daya daga cikin nasarorin da ya samu a matsayinsa na shugaban samari na kwamitin rijista da tabbatar da 'yan jam'iyya.

Kwamishinan labarai, Kinsley Fanwo ya sanar da manema labarai cewa tabbas gwamnan ya furta hakan, The Punch ta wallafa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel