Fani-Kayode ya tunkare ni da batun sauya sheka zuwa APC, Yahaya Bello

Fani-Kayode ya tunkare ni da batun sauya sheka zuwa APC, Yahaya Bello

- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce sn tattauan batun sauya sheka da tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode

- An ga gwamnan yana furta hakan ne a wani bidiyo inda ya bayyana cigaban da ya samar wa wa jam'iyyar a ranar Laraba

- Kwamishinan labaran jihar, Kingsley Fanwo, ya tabbatar wa da manema labarai cewa Gwamna Bello da kansa ya furta hakan

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce sun tattauna batun sauya sheka da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, daga jam'iyyar PDP ya koma jam'iyyar APC.

A wani bidiyo da aka daura a taron jam'iyyar APC da aka yi a jihar Kogi wanda aka saki a kafar sada zumunta ranar Laraba, Bello ya ce wannan yana daya daga cikin nasarorin da ya samu a matsayinsa na shugaban samari na kwamitin rijista da tabbatar da 'yan jam'iyya.

"Dan uwanmu kuma abokinmu, Chief Femi Fani-Kayode, ya koma jam'iyyar mu da kyakkyawan fata. Ya shigo jam'iyyar ne musamman don samar da cigaba wurin tabbatar da jam'iyyar ta bunkasa.

KU KARANTA: Sheikh Abduljabbar Kabara ya maka gwamnatin jihar Kano a gaban kotu

Fani-Kayode ya tunkare ni da batun sauya sheka zuwa APC, Yahaya Bello
Fani-Kayode ya tunkare ni da batun sauya sheka zuwa APC, Yahaya Bello. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

"Idan ba a manta ba Chief Femi Fani-Kayode babban jagoran jam'iyyar APC ne... Don haka ya yanke shawarar komawa jam'iyyar, ya tunkareni da batun, kuma zamu ba shi damar taka rawa a jam'iyyar," cewar gwamnan.

Kwamishinan labarai, Kinsley Fanwo ya sanar da manema labarai cewa tabbas gwamnan ya furta hakan, The Punch ta wallafa.

"Bidiyon a bayyane yake," cewar kwamishinan bayan wakilinmu ya bukaci sanin gaskiya dan gane da bidiyon da yayita yawo.

KU KARANTA: Mai gidan haya ya lakadawa 'yar haya mugun duka, ta maka shi a gaban kotu

Sai dai Fani-Kayode ya ce har yanzu dan jam'iyyar PDP ne shi. Kamar yadda ya wallafa a Twitter ranar Laraba, "Duk da mun tattauna akan jam'iyyu da siyasar kasar nan, har yanzu ina nan a PDP."

A wani labari na daban, akdarun sojin saman Najeriya sun halaka 'yan bindiga masu tarin yawa a samamen da suka kai ta jiragen yaki a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Wannan samamen ya biyo bayan kisan gilla da 'yan bindiga suka yi wa sama da mutum 40 a kananan hukumomi 5 na jihar a cikin kwana biyu kacal.

Kamar yadda kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, yace an ga 'yan bindigan a Sabon Madada tare da shanu kuma an ragargaza su, Channels TV ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

iiq_pixel