Rundunar sojojin Najeriya ta karyata cewar 'yan ta'adda sun kashe sojoji 20 a arewa maso gabas

Rundunar sojojin Najeriya ta karyata cewar 'yan ta'adda sun kashe sojoji 20 a arewa maso gabas

- Rundunar Sojin Najeriya ta musanta rahoton cewa an kashe sojoji 20 a yankin arewa maso gabas

- Rundunar sojojin ta ce babu abu makamancin haka da ya faru, inda ta kara da cewa wannan dabara ce da nufin karya gwiwar jama'a da kuma karya lagon sojoji

- Kakakin rundunar sojin, Birgediya Janar Mohammad Yerima ya ce rahoton ba gaskiya bane

Rundunar Sojin Najeriya ta karyata wani rahoton kafafen yada labarai na cewa 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP sun kashe sojoji 20 a arewa maso gabas.

An bayyana rahoton a matsayin karya, na bogi, kuma mara tushe wanda aka tsara shi da nufin karya gwiwar jama'a da kuma karya lagon dakarun sojin a kokarin da suke yi wajen yaki da ta’addanci, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Jihohin Najeriya 11 da basu jawo hankalin masu saka hannun jari na kasashen waje ba a cikin shekaru 2

Rundunar sojojin Najeriya ta karyata cewar 'yan ta'adda sun kashe sojoji 20 a arewa maso gabas
Rundunar sojojin Najeriya ta karyata cewar 'yan ta'adda sun kashe sojoji 20 a arewa maso gabas hOTO: @thecableng
Source: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa kakakin rundunar soji, Birgediya Janar Mohammad Yerima ne ya fayyace gaskiyar a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 11 ga Fabrairu, a Abuja.

A cewar Yerima, babu hari makamancin haka inda aka kashe sojoji 20, inda ya kara da cewa tawagar MSTs da tawagar bataliya 156 sun kakkabe harin da aka kaiwa dakarun.

Ya ci gaba da bayanin cewa tuni biyu daga cikin sojojin da suka samu raunuka suka fara karbar magani.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe jami’in dan sanda sannan suka raunata wasu 4 a Taraba

Jiragen Dakarun Sojojin Saman Nigeria, NAF, a ranar Laraba sun halaka yan bindiga masu yawa a mabuyarsu da ke dazukan jihar Kaduna, The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan tsaron da harkokin cikin gida, Mista Samuel Aruwan, ya lissafa wurarren da jiragen suka kai hari inda suka hada da Rahama, Tami, Sabon-Birni, Galadimawa da Ungwan Farinbatu.

Saura sun hada da Sabuwa, Kutemeshi, Gajere, Sabon Kuyello, Dogon-Dawa, Ngade Allah, Kidandan da kuma wasu garuruwan da ke kananan hukumomin Birnin-Gwari da Giwa a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel