‘Yar wasar fim ta ba maza shawarar auren mata rututu domin su daina bin matan banza

‘Yar wasar fim ta ba maza shawarar auren mata rututu domin su daina bin matan banza

- ‘Yar wasan fim, Grace Ifemeludike, ta yi tir da abin da ma’aurata su ke yi

- Grace Ifemeludike ta ce maza su na yawan fitsara da matan banza a waje

- Jarumar wasan kwaikwayon ta bada shawarar halatta auren mata rututu

‘Yar wasar fim, Grace Ifemeludike, ta ba mazan da su ke yaudarar matan aurensu shawarar su rungumi auren mata da yawa domin su daina lalata da mata.

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Daily Nigerian, Grace Ifemeludike wanda jarumar Nollywood ce, ta yi wannan kira ne a shafinta na Instagram.

Da ta ke magana a ranar Talata, 9 ga watan Fubrairu, 2021, Grace Ifemeludike, ta yi Allah-wadai da yadda zina ta zama ruwan dare tsakanin mazaje a Afrika.

‘Yar wasan ta bayyana lalatar da ake yi da cewa ‘abin takaici’ ne, ta alakanta lamarin da rashin tarbiyya.

KU KARANTA: Al’umma na son jin ko ‘kalau; An dade ba a ga Mai dakin Buhari ba

“Da alamu wannan lamari na ‘yan mata su rika bin mazan aure ya na kara kamari a al’ummarmu.” Inji Grace Ifemeludike.

“Mutane sun daina ganin abin da ake yi ba daidai ba ne, sun koma maganar wanda ya kamata a gani da laifin wannan shaidanci; mai gidan ko budurwar wajen."

"Tambayar da na ke yi, ina halayenmu na kwarai, da tarbiyya da koyarwar addinin kiristanci? Meyasa mu ke yaudarar kanmu a Afrika.” Inji Chioma Ifemeludike.

Ifemeludike ta cigaba da cewa: “Idan mace daya ba ta aiki, me zai hana mu yarda a rika auren mata da yawa, a maimakon daure gindi a rika fasikanci da cin amana.”

‘Yar wasar fim ta ba maza shawarar auren mata da yawa domin su daina bin matan banza
Chioma Chioma Ifemeludike Hoto: dailynigerian.com
Source: UGC

KU KARANTA: Wata kungiya ba ta yarda a haramta mu’amalar da cryptocurrencies ba

Ta ce: “A matsayinka na namiji, idan mace daya ba za ta yi maka, ka yi magana da mai dakinka, ku fahimci juna, a maimakon ka bi matan banza, sai ka je ka kara aure.”

A karshe tauraruwar ta yi kira ga ‘yan mata su daina fitsara a gari, su nemi mazaje, su yi aure.

Kwanakin baya kun ji labarin wata mata da ta rabu da mijinta, ta auri 'dansa 'dan shekaru 21, ta ce har sai da aka yi mata tiyata ta kwaskwarima domin ta kara kyau.

Marina Balmesheva, mai shekaru 35, wanda ta ke rubutu a kan motsa jiki, ta na dauke da juna biyu na mai tsohon gidanta, amma ta bukaci a raba wannan auren na su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel