An yanke wa wani barawon janareto daurin watanni 3 a gidan yari

An yanke wa wani barawon janareto daurin watanni 3 a gidan yari

- Wata kotu a jihar Kaduna ta yankewa wani barawon janareto hukuncin watanni 3 a magarkama

- Bayan shigar da kararsa, an bayyana cewa mai gidan da aka yiwa satan ne ya kamashi

- Kotun ta daure wanda ake zargin kuma alkalin bai bada damar yin belin barawon ba

Wata Kotun Majistare da ke Kaduna a ranar Alhamis ta yanke wa wani magini mai shekaru 25, Timothy David, hukuncin daurin watanni uku a gidan yari saboda satar janareto, Vanguard News ta ruwaito.

An tuhumi David da haɗin gwiwa tare da yin sata.

Alkalin kotun, Mista Ibrahim Emmanuel, ya yanke wa David hukuncin ne bayan ya amsa laifin da ake tuhumar sa da shi.

Emmanuel, bai bai wa mai laifin hukuncin biyan tara ba.

Ya ce wannan hukuncin zai zama mai hana wadanda ke son aikata irin wannan laifi.

KU KARANTA: Filayen jirgin saman Najeriya suna daga cikin masu muni a duniya, in ji wata hukuma

An yanke wa wani barawon janareto daurin watanni 3 a gidan yari ba tara
An yanke wa wani barawon janareto daurin watanni 3 a gidan yari ba tara Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

Tun da farko, mai gabatar da kara, Insp. Chidi Leo, ya fadawa kotun cewa wani mutum, Kingsley Japhet na Malali dake jihar Kaduna, ya shigar da korafi a kan David a ofishin ‘yan sanda na Malali a ranar 5 ga Fabrairu.

Leo ya ce, wanda ake kara tare da wasu mutum biyu, a yanzu haka, suna gidan yari wanda ya ake karar ya tsallake shinge tare da sace janareton da kudin da ya kai N180,000.

Ya ce wanda mai shigar da karar ya kama David yayin da yake kokarin bude kofar shiga gidansa.

Leo ya ce sauran abokan satan sun tsere.

Mai gabatar da kara ya ce an mika wanda ake zargin ga 'yan sanda.

A cewarsa, laifin ya ci karo da sashi na 245 da 207 na kundin manyan laifuka na jihar Kaduna, 2017.

KU KARANTA: Makiyaya 4,000 sun yi hijra daga jihohin kudu zuwa jihar Kaduna

A wani labarin, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya fada a ranar Litinin cewa cin hanci da rashawa ya ci gaba a kasar ne saboda wadanda suka bayyana barayi ba a daure su ko kuma hukunta su, jaridar The Punch ta ruwaito.

Amaechi, wanda ya yi magana a lokacin da yake gabatar da lacca ta 2021 na Jami’ar Fatakwal, ya bukaci jama’a su daina yin bikin girmama mutanen da suka wadata kansu ta hanyar satar dukiyar jama’a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.