'Yan fashi sun kashe wani ango wata daya bayan aurensa.

'Yan fashi sun kashe wani ango wata daya bayan aurensa.

- Wata matar da aka kashe mijinta ta bayyana yadda 'yan fashi suka mayar da ita bazawara

- Tace, 'yan fashin sun afkawa gidansu cikin dare daga bisani suka harbe mijinta

- Ta kuma bayyana yadda aka cafke wadanda suka aikata mummunan aikin kashe mijin nata

Wata matar mai suna Ramatu Idris da ke Unguwar Malam Lamu, Tankarau, Unguwar Dutsen Abba da ke karamar Hukumar Zariya, ta bayyana yadda ’yan fashi suka sanya ta zama bazawara bayan wata daya da aurenta da marigayi Yusuf Suleiman.

Idris ya fadawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Alhamis cewa lamarin ya faru ne a ranar 4 ga Fabrairu, da misalin karfe 12:45 na rana, kwanaki 28 bayan aurenta da Suleiman, The Nation ta ruwaito.

“Sun kasance kusan su bakwai ('yan fashin). Sun afka cikin gidanmu da karfi rike da bindigogi da sanda.

KU KARANTA: An kusa bada umarnin hada NIN da BVN na asusun bankin 'yan Najeriya, Dr Pantami

“Ni da mijina mun je ganin abin da ke faruwa a kan jin hayaniya da ihun neman taimako, sai kawai aka harbe shi a wuya a gabana kuma ya mutu nan take.

Ramatu, wanda lamarin ya rutsa da ita, ta yi ikirarin wadanda suka kashe mijinta masu aikata laifuka ne da suka kai samame gidan Alhaji Abdulaziz Sani, Kansilan da ke wakiltar Unguwar Dutsen Abba, suka yi awon gaba da ’yan uwansa shida.

Ta ce daga baya ne jami'an hukumar kula da sintiri na jihar Kaduna (KADVS) suka samu nasarar cafke 'yan fashin a kauyen Unguwan Mai Turmi, da ke karamar hukumar Igabi.

A halin da ake ciki bayan harin da aka kaiwa gidan Sani da kisan Suleiman, mazauna Kampani da Saye a Unguwar Dutsen Abba, sun roki Gwamnatin Jihar Kaduna da ta tura karin jami’an tsaro a kan hanyoyi a yankin don magance satar shanu, satar mutane da sauran laifuka.

KU KARANTA: Filayen jirgin saman Najeriya suna daga cikin masu muni a duniya, in ji wata hukuma

A wani labari, Sakamakon umarnin fatattakar makiyaya masu aikata laifuka a wasu jihohin kudu, kimanin makiyaya 4,000 sun bar jihohin kudu zuwa Kaduna, Nigerian Tribune ta ruwaito.

An tattaro cewa makiyayan tun makon da ya gabata suna dawowa zuwa garin Labduga, karamar hukumar Kachia, jihar Kaduna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.