Jihohin Najeriya 11 da basu jawo hankalin masu saka hannun jari na kasashen waje ba a cikin shekaru 2
Tsawon shekaru biyu, jihohi 11 daga cikin 36 a Najeriya sun kasa jawo hankalin masu saka jari daga kasashen waje, jaridar The Cable ta ruwaito, inda ta ambaci hukumar kididdiga ta kasa (NBS) a matsayin maiyarta.
Legit.ng ta tattaro cewa jihohi 11 da lamarin ya shafa basu sami damar jawo hankalin ko wani mai saka jari daga kasashen waje ba a cikin shekarar 2019 da 2020, a cewar rahoton shigo da kaya kasar nan da NBS ta wallafa kwanan nan.
KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe jami’in dan sanda sannan suka raunata wasu 4 a Taraba
Ga jerin jihohin da basu ja hankalin masu saka hannun jari ba a kasa:
1. Bayelsa
2. Ebonyi
3. Ekiti
4. Gombe
5. Jigawa
6. Kebbi
7. Kogi
8. Plateau
9. Taraba
10. Yobe
11. Zamfara
KU KARANTA KUMA: Kuma dai: Boko Haram sun kai hari a garin Geidam, sun yi awon gaba da wasu jami'an kwastam 3
A baya mun ji cewa Legas ta kasance jihar Najeriya mafi soyuwa ga masu saka hannun jari yayin da take kan gaba a jerin jihohin da suka fi jawo hankulan masu saka jari a shekarar 2020 inda ta zarce sauran jihohin kasar ciki harda Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Legit.ng ta lura cewa rahoton wanda ya ambaci Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) a matsayin tushensa, ya nuna cewa Legas, cibiyar kula da tattalin arzikin Najeriya, ta jawo dala biliyan 8.31 a hannun jari.
Wannan ya wakilci kaso 85.7 na jimillar jarin da ya shigo kasar nan a shekara ta 2020.
1. Lagos - $ 8.31 biliyan 2. Abuja (FCT) - dala biliyan 1.27 3. Abia - $ 56.07 miliyan 4. Niger - $ 16.36 miliyan 5. Ogun - $ 13.39 miliyan 6. Anambra - $ 10.02 miliyan 7. Kaduna - $ 4.03 miliyan 8. Sakkwato - $ 2.50 miliyan 9. Kano - $ 2.38 miliyan 10. Akwa Ibom - $ 1.05 miliyan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng