Kuma dai: Boko Haram sun kai hari a garin Geidam, sun yi awon gaba da wasu jami'an kwastam 3
- Mayakan Boko Haram sun sake yin barna a garin Geidam da ke jihar Yobe
- An yi garkuwa da jami'an kwatsam uku a yayin harin da aka kai kusa da iyakar Najeriya
- Kakakin yan sandan jihar ya tabbatar da satar jami’an wanda aka aiwatar a ranar Talata,9 ga watan Fabrairu
Wani rahoto da jaridar Premium Times ta fitar ya nuna cewa mayakan Boko Haram sun sace akalla jami’an hukumar kwastam ta Najeriya uku a ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu, a garin Geidam da ke jihar Yobe.
Legit.ng ta tattaro cewa maharan sun kwashe jami’an ne yayin wani hari da suka kai wa garin da ke kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar da yammacin ranar Talata.
KU KARANTA KUMA: Saka hannun jari: Jerin sunayen jihohi 10 da suka fi arziƙi a Nigeria a 2020
Da suke zantawa da dandalin labaran na yanar gizo, majiyoyin tsaro sun ce maharan bayan sun shiga cikin garin ta hanyar Geidam sun kwashi jami'an da aka girke a shingen binciken ababen hawa a kan hanyar.
Da yake martani a kan lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Yobe, Dungus Abdulkarim ya tabbatar da harin na Geidam.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya ce ba a samu asarar rai ko daya ba, ya kara da cewa' yan ta'addar sun kona motar babban asibitin Geidam, sannan suka sace kayayyakin wani shago.
‘Yan ta’addan Boko Haram sun kai mamaya garin a ranar Laraba, 6 ga watan Janairu, inda suka fara harbi ba kakkautawa, abin da ya haifar da tsoro.
Wani ganau ya ce an fasa shagunan garin sannan aka kwashe kayan abinci kafin aka cinna musu wuta.
KU KARANTA KUMA: Ka tsaya a layinka, hadimin Buhari ga Fani-Kayode bayan ya karyata batun komawarsa APC
A gefe guda, 'Yan bindiga a ranar Laraba sun halaka mutane uku a garin Nkpor da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambara.
Premium Times ta ruwaito cewa wasu yan bindigan kimanin su biyar ne suka bi wadanda suka riga mu gidan gaskiyar zuwa wani wurin da ake taron jin ra'ayin mutane.
An tattaro cewa mutane ukun masu dauke da bindigun, da isarsu wurin taron sun tafi kai tsare wurin mutane ukun suka bindige su daga kusa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng