Yan bindiga sun kashe jami’in dan sanda sannan suka raunata wasu 4 a Taraba

Yan bindiga sun kashe jami’in dan sanda sannan suka raunata wasu 4 a Taraba

- Yan bindiga sun kai hari wata tashar bincike na yan sanda a karamar hukumar Takum na jihar Taraba

- Maharan sun kuma kashe wani jami'in dan sanda tare da raunata wasu masu tafiya hudu

- Lamarin ya afku ne a ranar Laraba, 10 ga watan Fabrairu

Rahotanni sun kawo cewa wani jami’in dan sanda ya rasa ransa a jiya Laraba, 10 ga watan Fabrairu, yayinda yan bindiga suka kai hari wata tashar bincike na yan sanda a kauyen Chanchanji da ke karamar hukumar Takum na jihar Taraba.

Majiyoyi sun bayyana cewa yan bindigar wadanda suka zo kan babura, sun bude wuta a kan jami’an yan sandan da ke kula da tashar binciken, inda suka kashe wani jami’i yayinda wasu masu tafiya hudu suka ji raunuka a harin.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa yan bindigan sun tsere da bindigar jami’in da suka kashe.

Yan bindiga sun kashe jami’in dan sanda sannan suka raunata wasu 4 a Taraba
Yan bindiga sun kashe jami’in dan sanda sannan suka raunata wasu 4 a Taraba Hoto: @PremiumTimesng
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Kuma dai: Boko Haram sun kai hari a garin Geidam, sun yi awon gaba da wasu jami'an kwastam 3

Wani mazaunin Chanchanji ya ce yan bindigan, wadanda suka shigo daga jihar Benue sun bude wuta a tashar binciken da ke cike da yan sanda, inda suka kashe wani jami’i da ke bakin aiki.

Ya ce: “Yan bindigan sun zo a kan babura uku sannan suka kwaso da gudu zuwa gadar da misalin karfe 6:50 na safe.

“Bayan dan wani lokaci, sai muka ji karar harbi, amma saboda rashin tsaron da ke wajen, bamu yi gaggawan zuwa yankin ba. Sai bayan mintuna 30 sannan muka je wajen sai kawai muka ga an kashe jami’in dan sanda a harin.

“Wasu mutum hudu, harda dan Gara na Chanchanji sun jikkata a harin.”

Mazaunin yankin ya kuma ce matasan Jukun na zargin yan bindigan na iya kasancewa yan Tiv ne ke ramuwar gayya.

Kakakin yan sandan jihar Taraba, Reform Leha, wanda ya tabbatar da harin a wayar tarho, ya ce: “Eh, an kashe wani jami’in dan sanda da ke aiki na musamman a yankin a harin sassafen.

“Yan gudun hijira hudu sun jikkata, Wadanda suka jikkata na samun sauki a babban asibitin Takum."

KU KARANTA KUMA: Jaruman Sojojin Najeriya sun dakile harin yan Boko Haram, sun kashe 19

A gefe guda, bidiyon wata matashiyar yarinya tana yakar 'yan fashi da makami wadanda suka shiga shagonsu suna barazana ga mahaifiyarta ya karade kafafen sada zumuntar zamani.

Mummunan lamarin ya faru ne a yankin Uribe Uribe da ke Bagota, babban birnin Colombia a ranar Alhamis, 4 ga watan Fabrairu lokacin da wani a babur ya tsaya a shagon sannan ya kutsa ciki da karfe 4am.

Mai shagon tana da yara mata biyu masu shekaru biyu da 14 kuma suna cikin shagon a yayin da dan fashin ya kai harin, The Nation ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel