Bidiyon jarumar yarinya tana fatattakar kattin 'yan fashi daga shagon mahaifiyarta da adda

Bidiyon jarumar yarinya tana fatattakar kattin 'yan fashi daga shagon mahaifiyarta da adda

- Wata yarinya mai shekaru 14 ta gwada jarumta tare da nuna kaunar mahaifiyarta a fili

- Matashiyar budurwar ta fatattaki 'yan fashin da suka kai wa shagon mahaifiyarta hari da adda

- Amma duk da haka sun yi nasarar harbin mahaifiyarta wanda babu jimawa aka shawo kan matsalar domin bata jigata sosai ba

Bidiyon wata matashiyar yarinya tana yakar 'yan fashi da makami wadanda suka shiga shagonsu suna barazana ga mahaifiyarta ya karade kafafen sada zumuntar zamani.

Mummunan lamarin ya faru ne a yankin Uribe Uribe da ke Bagota, babban birnin Colombia a ranar Alhamis, 4 ga watan Fabrairu lokacin da wani a babur ya tsaya a shagon sannan ya kutsa ciki da karfe 4am.

Mai shagon tana da yara mata biyu masu shekaru biyu da 14 kuma suna cikin shagon a yayin da dan fashin ya kai harin, The Nation ta wallafa.

KU KARANTA: Mata karkatar da hankali suke yi, Lauyan da yayi soyayya da mata fiye da 100

Bidiyon jarumar yarinya tana fatattakar kattin 'yan fashi daga shagon mahaifiyarta da adda
Bidiyon jarumar yarinya tana fatattakar kattin 'yan fashi daga shagon mahaifiyarta da adda. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Bidiyon lamarin wanda CCTV ta cikin shagon ta nada ya nuna wani mutum sanye da bakaken kaya da kuma bakar malfa, ya shiga shagon inda ya nufa wurin karbar kudi.

Zakakura kuma jarumar yarinyar an ganta ta fuskanci dan fashin inda take masa barazana tare da nuna masa adda.

Ta wurga addar a iska inda hakan yasa dan fashin yayi hanyar gaban shagon domin arcewa.

Wani dan fashin ya bayyana a cikin shagon don taimakon dan uwansa amma ta fatattakesu inda su biyun suka bar shagon tare da hayewa babur dinsu suka karawa bujensu iska.

Kamar yadda rahotannin suka bayyana, wadanda ake zargin sun harba mahaifiyar yarinyar kafin su bar shagon.

An gaggauta mika ta asibiti inda aka samu shawo kan matsalar babu bata lokaci.

KU KARANTA: Muna da sabbin dabarun yakar ta'addanci da 'yan bindiga a kasar nan, Osinbajo

A wani labari ma daban, majalisar jihar Bauchi ta amince da sauya sunan jami'ar jihar Bauchi zuwa Jami'ar Sa'adu Zungur.

Dr Aliyu Tilde, kwamishinan ilimi na jihar ya sanar da cewa nan babu jimawa zai fara aikin sauyin sunan.

Kamar yadda Dr Tilde ya sanar, gwamnatin tana cigaba da gwagwarmaya tare da Saudi Arabia wurin bautawa kasar nan ta hanyar koyarwar marigayi Malam Sa'adu Zugur wanda dan asalin jihar Bauchi ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel