Jaruman Sojojin Najeriya sun dakile harin yan Boko Haram, sun kashe 19
- Sojoji sun samu nasarar kawar da yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno
- Wannan ya biyo bayan harin da yan ta'addan suka kai Askira Uba
- A cewar majiya, an kashe yan ta'adda kimanin guda 20
Dakarun Sojojin Najeriya a ranar Talata sun kawar da harin yan ta'addan ISWAP a Rann, jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya bayan ruwan harsasai da jirage.
Rann, hedkwatar karamar hukumar Kala Balge, na iyaka da kasar Kamaru.
Bayan batakashi da yan ta'addan, Sojojin tare da mayakan sama sun hallaka yan ta'adda 19 cikin motocin yaki 5.
A cewar PRNigeria, yan ta'addan sun dira Rann ne misalin karfe 6 na yamma cikin motocin yaki takwas da babura inda suke kokarin kai hari barikin Sojojin 3 Brigade.
"Yayin harin, an ragargaji motocin yakin yan ta'addan Boko Haram, da wadanda ke ciki," jaridar ta nakalto da wata majiya.
"An hallaka yan ta'adda da dama sakamakon ruwan bama-bamai daga jiragen sama da kuma harsasai daga Sojojin kasan Najeriya."
"Akalla gawawwakin yan Boko Haram 19 aka gano a wajen, tare da motocin yakinsu, ban wadanda ke cikin daji."
DUBA NAN: An kusa bada umarnin hada NIN da BVN na asusun bankin 'yan Najeriya, Dr Pantami
DUBA NAN: Jihohi 10 da masu kudi suka fi sanya hannun jari shekarar 2020, 5 na Arewa
A bangare guda, a ranar Laraba, 10 ga watan Fubrairu, 2021, majalisar dattawa ta fada wa jami’an tsaro suyi amfani da jiragen yaki domin bankado ‘yan bindigan da ke jeji.
Jaridar Punch ta ce shugaban majalisar dattawan kasar, Ahmad Ibrahim Lawan ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayanin matsayar da majalisa ta dauka.
Sanatoci irinsu Tolulope Odebiyi, Solomon Adeola, Ademola Balogun, da Ali Ndume su ka ce akwai bukatar ayi wani abin game da sha’anin tsaro a kasar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng