IPPIS zamba ne, gwamnati ta yaudare mu ne kawai, inji wani shugaban NASU

IPPIS zamba ne, gwamnati ta yaudare mu ne kawai, inji wani shugaban NASU

- Kungiyar ma'aikatan jami'a ta NASU ta bayyana rashin jin dadinta dangane da IPPIS

- Kungiyar ta kira IPPIS zamba, kuma mummunan yaudara daga gwamnatin tarayya

- Kungiyar ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta zambace su ne kawai domin su shiga tsarin

Shugaban kungiyar ma'aikatan jami'a reshen jami'ar Lagos, Mista Kehinde Ajibade, ya bayyana tsarin hadakar ma'aikata game da biyan albashi (IPPIS) da ake biyan ma'aikatan gwamnati a matsayin yaudara., The Nation ta ruwaito.

Ya zargi Gwamnatin Tarayya da yaudarar kungiyar don sanya hannu a kanta.

NASU da kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU) sun fara yajin aiki na ba-sani-ba-sabo a ranar Juma’ar da ta gabata don nuna rashin amincewa da yadda ake gudanar da ayyukan na tsarin IPPIS da kuma rashin biyan basussukan alawus-alawus, da sauransu.

“IPPIS zamba ne; yaudara ce; a zahiri ba mai ɗorewa bane a cikin tsarin jami'a. Wannan ita ce gaskiya saboda mun gano cewa gwamnatin tarayya kawai ta yaudare mu ne don mu shiga wannan dandalin,” ya ce a wata hira.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa za ta tattauna kan rikicin makiyaya Fulani ranar Talata

IPPIS zamba ne, gwamnati ta yaudare mu ne kawai, inji wani shugaban NASU
IPPIS zamba ne, gwamnati ta yaudare mu ne kawai, inji wani shugaban NASU Hoto: Vanguard News
Source: UGC

Da yake bayar da cikakkun bayanai game da mummunan ayyukan da IPPIS din ke yi, Ajibade ya ce da yawa daga cikin mambobin kungiyar an sauya su saboda IPPIS ba ta biyan cikakken albashin su, tana cire kudaden kungiyar ba tare da nuna bambanci ba.

Ajibade ya ce kungiyar za ta ci gaba da yajin saboda gwamnati ba ta da gaskiya. Ya ce gwamnatin ta yi watsi da yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar kwadago kuma ba ta magance batutuwan da ta gabatar ba kamar yadda ta yi alkawari.

Sauran batutuwan da kungiyar NASU ke son gwamnati ta magance su ne - rashin biyan kudaden fansho ga wadanda suka yi ritaya, da rashin biyan bashin mafi karancin albashi da aka biya wasu ma’aikatu, sassa da hukumomi.

Hakanan ta yi watsi da tsarin raba kashi 75-25 na alawus din da aka samu a madadin ASUU, inda ta nemi gwamnati da kar ta hada kungiyar da wasu.

KU KARANTA: Watanni 5 bayan turawa Rarara kudade, har yanzu batun wakar Buhari shiru

A wani labarin, Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya ce, Najeriya za ta bukaci samar da guraben aiki miliyan 5 a kowace shekara har tsawon shekaru 10 don cike gibin rashin aikin yi, Premium Times ta ruwaito.

A cikin wani rahoto a ranar Litinin, asusun ya ce samar da wannan adadin ayyukan zai cimma burin kirkirar ayyuka da suka kai miliyan 54 a cikin shekaru goma masu zuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel