Gwamnati ta daskare asusun bankin Sunday Igboho, ya yi martani
- Dan gwagwarmayar yarbawa Sunday Igboho dya gargadi gwamnatin tarayya da ta saki asususun bankinsa
- Dan gwagwamayan ya zargi gwamnatin tarayya da gargame asusunsa ba tare da laifi ba
- Yace ko dai gwamnati ta bada umarnin bude asusunsa ko kuma ya dauki matakin da ya dace
Shahararren mai rajin kare hakkin Yarbawa Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya zargi Gwamnatin Tarayya da daskarar da asusun ajiyarsa na banki, The Nation ta ruwaito.
Ya ce an dauki matakin daskararwar ne saboda yakin da yake yi da masu kashe-kashe a yankin Kudu maso Yamma.
Igboho ya yi zargin cewa Gwamnatin Tarayya ta dakatar da asusun ajiyar sa na banki saboda wasu mutane na karbar gudummawa a madadin sa.
KU KARANTA: Ya kamata Buhari ya dama da Inyamurai a nadin hafsoshi, in ji Yarbawa
Ya musanta cewa ba shi da wata alaka da gudummawar, yana mai gargadin cewa dole ne a bude asusunsa domin kauce wa zanga-zangar da matasa ke yi a fadin yankin Kudu maso Yamma.
A kalaman nasa: “Sun daskarar da asusuna na banki saboda ina yaki kan tafarkin adalci. Na san Yarbawa suna baya na.
“Ba zan hakura ba. Dole ne in cimma burina ta hanyar kawo karshen laifuka a kasar Yarbawa.
“Idan suka ki sakin asusuna, za a yi zanga-zanga mai tsanani a duk yankin Kudu maso Yamma.
“Eh, Yarbawa na rayuwa cikin tsoro. Suna tsoron kada makiyayan su kashe su.”
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: WTO za ta nada Darakta-Janar a ranar Litinin mai zuwa
A wani labarin, Gwamnoni a Arewa a ranar Talata sun bayyana batun kiwo a fili da makiyaya suke yi a matsayin tsohon abu. Ya kamata ya kare, The Nation ta ruwaito.
Wannan shawarar ita ce sakamakon, taron kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya, wanda aka gudanar.
Shawarar ta yi daidai da ra'ayin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, wanda ya ce ya kamata makiyaya su rungumi kiwo a waje daya su daina kiwon shanun su daga Arewa zuwa Kudu shi ne zaman lafiya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng