Watanni 5 bayan turawa Rarara kudade, har yanzu batun wakar Buhari shiru

Watanni 5 bayan turawa Rarara kudade, har yanzu batun wakar Buhari shiru

- A baya watanni biyar da suka shude, mawaki Rarara ya bukaci a tura masa kudi don yi wa Buhari waka

- 'Yan Najeriya sun amsa kiranshi, yayin da suka tura kudaden kuma suka nuna a kafafen yada labarai

- Sai dai, Rarara yace ya yi haka ne dan gwada farin jinin Buhari a wajen talakawan Najeriya

Watanni biyar bayan neman 'yan Najeriya su dauki nauyin waƙarsa ta gaba a kan Shugaba Muhammadu Buhari, har yanzu babban mawaki, Dauda Kahutu Rarara bai fitar da wata waƙa ba, Daily Trust ta ruwaito.

Rarara ya kasance, a watan Satumbar 2020, ya roki ‘yan Nijeriya da su ba da gudummawar N1,000 kowannensu don daukar nauyin waƙarsa ta gaba ga Shugaba Buhari don ya nuna wa duniya cewa har yanzu shugaban ya fi son talakawa.

Tun daga wannan lokacin, mutane ke ta yin tambayoyi ko mawaƙin ya gaza samun adadin da ake buƙata ko kuma yunƙurin kawai ƙoƙari ne na yaudarar talakawa.

A daya daga cikin tattaunawar da mawakin ya gudanar a kan shirin nasa, an ruwaito Rarara yana cewa: “Na yi wannan kiran saboda wani ikirarin da masu adawa da Buhari suka yi na cewa Buhari ya rasa farin jini a wajen talakawan Najeriya.

KU KARANTA: Zulum da wasu sun isa Kamaru, don dawo da 'yan gudun hijirar Najeriya 9,800

Watanni 5 bayan turawa Rarara kudade, har yanzu batun wakar Buhari shuru
Watanni 5 bayan turawa Rarara kudade, har yanzu batun wakar Buhari shuru Hoto: Premium Times
Asali: UGC

“Sanin sarai cewa Shugaba Buhari har yanzu masoyi ne ga talakawan Najeriya, na yanke shawarar yin kira ga magoya bayan Shugaban Kasa da su ba da gudummawar Naira 1000 kowannensu don daukar nauyin waka ta ta gaba.

“Wannan kawai don a lalata farfagandar cewa talakawa ba sa tare da Buhari ne. Ta hakan, idan suka amsa kiran suka kuma dauki nauyin aikin, hakan na nufin shugabanmu har yanzu yana da farin jini kuma har yanzu talakawan Najeriya suna bayansa.”

Dukkan ƙoƙari don samun jin ta bakin mawaƙin ya ci tura saboda duk kiran da aka yi wa layin wayarsa ba a samunsa.

Duk da haka, da yawa daga masu lura da al'amura sun nuna bacin ransu game da rashin mawakin na yin abin da ya alkawarta da kuma rashin fitowa fili ya bayyana tare da bayyana jimillar kudin da ya tara kamar yadda ya yi alkawari.

KU KARANTA: Gwamnati ta daskare asusun bankin Sunday Igboho, ya yi martani

A wani labarin, Wasu dattawa daga yankin Kudu maso Yamma a ranar Talata sun yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari kan nadin daya daga cikin ’ya’yansu a matsayin Babban Hafsan Sojin Sama, Daily Trust ta ruwaito.

Dattawan, a karkashin inuwar taron kungiyar dattawan Yarbawa, sun ce karimcin da shugaban ya nuna ya nuna matukar amincewarsa da Kudu maso Yamma don taimakawa gwamnatinsa ta bai wa ’yan Najeriya tsaron da ake matukar bukata kamar yadda ya yi alkawari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel