Daukar ayyuka miliyan 5 duk shekara na shekaru 10 ne mafita ga Najeriya, IMF

Daukar ayyuka miliyan 5 duk shekara na shekaru 10 ne mafita ga Najeriya, IMF

- Don rage radadin rashin aikin yi a Najeriya, IMF ta bada rahoton ta kan mafita ga kasar

- IMF ta bayyana cewa akwai bukatar daukar ayyuka miliyan 5 duk shekara na tsawon shekaru 10

- IMF ta bayyana cewa hakan ne kadai mafita ga karuwar rashin aikin yi a Najeriya

Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya ce, Najeriya za ta bukaci samar da guraben aiki miliyan 5 a kowace shekara har tsawon shekaru 10 don cike gibin rashin aikin yi, Premium Times ta ruwaito.

A cikin wani rahoto a ranar Litinin, asusun ya ce samar da wannan adadin ayyukan zai cimma burin kirkirar ayyuka da suka kai miliyan 54 a cikin shekaru goma masu zuwa.

Asusun ya kuma ce al’ummar kasar na bukatar rungumar bude kofa ga waje da kuma kyawawan manufofi don farfado da ci gaban kasar.

Adadin rashin aikin yi a Najeriya ya tashi zuwa 27.1% a zango na biyu na shekarar 2020, inda ya karu daga 23.1% a cikin zango na uku na shekarar 2018.

KU KARANTA: Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC kan zaben 2023 mai zuwa

Daukar ayyuka miliyan 5 duk shekara na shekaru 10 ne mafita ga Najeriya, IMF
Daukar ayyuka miliyan 5 duk shekara na shekaru 10 ne mafita ga Najeriya, IMF Hoto: The Guardian
Source: UGC

Babban mawuyacin halin rashin aikin yi, wanda wasu ke ganin ya fi tsanani fiye da yadda aka ruwaito, ya zama mafi muni ta hanyar annobar coronavirus, wanda ya haifar da rufe harkokin kasuwanci.

IMF ta ce "Najeriya za ta bukaci kirkirar sabbin ayyuka akalla miliyan 5 a kowace shekara idan aka kwatanta da kusan asarar miliyan biyu na rashin aiki a kowace shekara a cikin shekaru biyar da suka gabata," in ji IMF din a cikin rahotonta na IV da ta gabatar kan Najeriya.

Asusun na IMF ya ba da shawarar a yi amfani da Yarjejeniyar Cinikin Kasashen Nahiyar Afirka (AfCFTA) don magance rashin aikin yi.

AfCTA na shirin kafa kasuwa guda daya, bunkasa gasa tsakanin kasashen Afirka, zurfafa hadewar tattalin arziki, a cewar Kwamitin Tattalin Arzikin Majalisar Dinkin Duniya na Afirka, zai daga cinikayyar tsakanin Afirka da kusan 52% cikin 100% nan da shekarar 2022.

KU KARANTA: Sabon shugaban sojoji ya sake ziyartar jihar Borno a karo na biyu

A wani labarin, Mista Umar Ndashacba, Manajan Shirye-shirye na Shirin Ciyar da Makarantun Gida na Kasa (NHGSFP) a Neja, ya ce aƙalla an samar da ayyuka sama da 14,000 a cikin shekaru biyu da kasancewar shirin a jihar.

Ndashacba ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel