‘Yan Majalisa za su yi wa sababbin hafsoshin tsaron da Buhari ya nada tankade da rairaya

‘Yan Majalisa za su yi wa sababbin hafsoshin tsaron da Buhari ya nada tankade da rairaya

- Majalisar Wakilan Tarayya za ta tantance nadin shugabannin sojojin Najeriya

- An kafa wani kwamiti mai dauke da ‘Yan Majalisa 20 da za su yi wannan aikin

- A baya, shugabannin Najeriya su na watsi da Majalisa wajen nada hafsun tsaro

Jaridar Daily Trust ta ce majalisar wakilan tarayya ta kafa wani kwamiti na musamman da zai tantance sababbin shugabannin tsaron Najeriya.

Majiyar ta ce shugabana kwamitin tsaro a majalisar wakilai, Honarabul Babajimi Benson ne zai shugabanci wannan sabon kwamitin da aka kafa.

An tada wannan kwamiti a majalisar tarayyar ne bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiko wa Femi Gbajabiamila takarda game da batun.

Wannan kwamiti na Hon. Babajimi Benson ya na kunshe da ‘yan majalisa biyar daga cikin kwamitocin tsaro, sojojin kasa, na sama da na ruwa.

KU KARANTA: Amao: Shugaba Buhari ya fada mana mu murkushe Boko Haram

Da Gbajabiamila ya ke karanto wasikar a zauren majalisa, ya ce Buhari ya dogara da sashe na 171(1), (2)(c) da 4 na tsarin mulki wajen nade-naden.

Shugaban kasa ya zabi sababbin hafsoshin sojojin kasa, na sama, na ruwa da shugaban hafsun tsaron.

Wadanda shugaba Buhari ya zaba su ne: Manjo Janar Lucky Irabor; Manjo Ibrahim Attahiru; Rear Admiral Auwal Gambo da Air Vice Marshal Isiaka Amao.

Akwai bukatar ‘yan majalisar Najeriya su tabbatar da wannan nadi da shugaban kasar ya yi a gidan soja, don haka ya bukaci majalisar ta tantance hafsoshin.

‘Yan Majalisa za su yi wa sababbin hafsoshin tsaron da Buhari ya nada tankade da rairaya
Sababbin hafsun Sojoji Hoto: @NgrPresident
Asali: Facebook

KU KARANTA: Aikin dogo Buhari ya maidawa masu suka martani, ya kare Gwamnatinsa

Kwanakin baya ne shugaba Buhari ya sauke Janar Gabriel Olonisakin; Laftanan Janar Tukur Buratai; Admiral Ibok Ibas; da Air Marshall Sadique Abubakar.

Kungiyar 'Alliance on Surviving COVID-19 and Beyond' ta soki nadin Hafsoshin tsaron da aka yi, ta ce ya kamata a aika sunayen hafsun sojoji zuwa gaban Majalisa.

Lauyoyin kungiyar sun ce a dokar kasa, sai ‘Yan Majalisa sun tantance hafsun sojojin da aka nada.

Femi Falana da kungiyarsa sun ce yin hakan shi ne abin da tsarin mulkin kasa da dokokin gidan soja ya ce. Daga baya, fadar shugaban kasa ta yi wa dokokin biyayya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel