Kungiyar Falana ta ce ya kamata a aika sunayen Hafsun sojoji zuwa gaban Majalisa

Kungiyar Falana ta ce ya kamata a aika sunayen Hafsun sojoji zuwa gaban Majalisa

- 'Alliance on Surviving COVID-19 and Beyond' ta soki nadin Hafsoshin tsaro

- Kungiyar tace shugaban kasa ya saba doka a wajen nadin wannan mukamai

- A dokar Najeriya, sai ‘Yan Majalisa sun tantance hafsun sojojin da aka zaba

Wata kungiya mai suna Alliance on Surviving COVID-19 and Beyond (ASCAP), ta soki yadda aka bi wajen nadin sababbin shugabannin hafsun sojoji a makon nan.

Wannan kungiya da Femi Falana yake jagoranta, ta ce ya kamata ace shugaban kasa ya tura sunayen sababbin hafsun tsaron zuwa ga ‘yan majalisar tarayya.

Kungiyar ta ce sai ‘yan majalisa sun tantance jami’an tsaron, sannan za a tabbatar da su a ofis.

Kamar yadda The Cable ta rahoto, jawabin kungiyar Alliance on Surviving COVID-19 and Beyond ya na cewa:

KU KARANTA: Tsaro ya tabarbare – Buhari ya fadawa sababbin Hafsun Sojojin Najeriya

"ASCAP ta gano cewa nadin bai yi ba saboda shugaba Muhammadu Buhari bai tura sunayen wadanda ya zaba zuwa majalisar tarayya domin a amince da su ba."

Femi Falana da kungiyarsa suka ce yin hakan shi ne bin tsarin mulkin kasa da dokokin gidan soja.

“An saba nada hafsun sojoji ba tare da an kai sunayensu gaban majalisa ba, haka ake yi tun 1999, wanda a 2008, Festus Keyamo SAN ya kalubalanci gwamnatin tarayya.”

A halin yanzu babban Lauya Festus Keyamo, Minista ne a gwamnatin Muhammadu Buhari, kuma shi ne ya yi galaba a kan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a kotu.

KU KARANTA: Maganganun mutane sun sa an yi waje da Shugabannin Soji

Kungiyar Falana ta ce ya kamata a aika sunayen Hafsun sojoji zuwa gaban Majalisa
Sababbin Hafsun Sojoji Hoto: Facebook @FemiAdesina
Asali: Facebook

"A hukuncin shari’ar mai lamba FHC/ABJ/ CS/611/2008 da aka yi a 2013, Alkali Adamu Bello J ya zartar da cewa shugaban kasa shi kadai bai da ikon nada hafsun sojoji."

Abin da sashe na 218 da sashe na 18 (1) & (3) na dokar sojojin kasa ta ce shi ne za a aika sunayen hafsun sojojin da aka zaba domin majalisa ta tantance su, inji ASCAP.

Gwamnatin tarayya ba ta daukaka wannan kara ba, don haka ASCAB ta ke bukatar Mai girma Muhammadu Buhari ya bi doka, ko kuma ya zama ya aika ba daidai ba.

Wadanda aka nada su ne: Manjo Janar Leo Irabor, Manjo Janar Ibrahim Attahiru Rear Admiral Auwal Z Gambo, da kuma Air Vice Marshall Isiaka O Amao.

Kugiyar Afenifere da tsohon shugaban Ndigbo, Nnia Nwodo, sun soki yadda aka nada hafsun tsaro ba tare da an zabo Sojan Ibo ba, su ka ce ana nuna son kai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel