Buhari: Abin da ya sa za mu gina titin jirgin kasa har zuwa Jamhuriyyar Nijar

Buhari: Abin da ya sa za mu gina titin jirgin kasa har zuwa Jamhuriyyar Nijar

- Shugaban Najeriya ya bayyana irin amfanin gina titin jirgin kasa zuwa Nijar

- Shiga da fice da kayan amfanin gona da ma’adani zai zo wa kasashen da sauki

- Muhammadu Buhari yace gwamnatin Najeriya za ta samu karin kudin shiga

A ranar Talata, 9 ga watan Fubrairu, 2021, shugaba Muhammadu Buhari ya fito ya kare matakin da ya dauka na gina titin dogo zuwa Jamhuriyyar Nijar.

Punch ta ce shugaban kasar ya maida martani ga masu sukar wannan katafaren aiki da ya kinkimo.

Mai girma Muhammadu Buhari ya ce kadan daga cikin amfanin gina titin jirgin kasa zuwa kasar Nijar shi ne zai bunkasa kasuwancin da ake yi a yankin sahara.

Shugaban kasa Buhari ya ce wannan aiki da za ayi, zai taimaka wa yarjejeniyar nan ta African Continental Free Trade Area da kasashen Afrika su ka sa wa hannu.

KU KARANTA: Abin da ya sa ake rashin gaskiya - Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi

A cewar shugaban kasar, ana kasuwanci sosai tsakanin Najeriya da makwabciyar ta Nijar a Jibiya da Maradi, an shafe tsawon daruruwan shekaru aru ana wannan.

Buhari ya ce aikin dogon zai taimaka wa mutanen Kano domin zai ratsa jihar. Sannan kuma ya bi ta manyan biranen Arewa irinsu Kazaure, Daura da kuma Katsina.

Idan an kammala wannan aiki, za a rika daukar fasinjoji da kayan amfanin gona da albarkatun ma’adanai zuwa kamfanoni har kudu ba tare da an sha wahala ba.

Da wannan jirgin kasa, za a rika shiga ko fita da kaya zuwa Nijar da Najeriya a cikin sauki.

KU KARANTA: Gwamna Dave Umahi ya jero wasu tarin alheran Buhari

Buhari: Abin da ya sa za mu gina titin jirgin kasa har zuwa Jamhuriyyar Nijar
Buhari ya na kaddamar da aikin dogon Kano-Maradi Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

A gefe guda, Najeriya za ta samu kudin shiga a dalilin fadada kasuwancin da ta yi. Mutanen Nijar kuma za su samu damar kasuwanci da hada-hada da makwabtansu.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne wajen bikin kaddamar da wannan aiki, wanda ya yi ta kafar yanar gizo daga ofishinsa da ke fadar shugaban kasa a Abuja.

Kun ji cewa bayan watanni biyar da amincewa da wannan gagarumin aiki a FEC, za'a fara ginin layin dogo daga Najeriya zuwa Nijar mai tsawon kilomita kusan 300.

Gwamnatin tarayya ta na kyautata zaton cewa wannan layin dogo zai inganta kasuwanci. A daidai lokacin da wasu su ke ganin za a yi asarar tulin kudi ne a banza.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel