Ya kamata Buhari ya dama da Inyamurai a nadin hafsoshi, in ji Yarbawa

Ya kamata Buhari ya dama da Inyamurai a nadin hafsoshi, in ji Yarbawa

- Kungiyar dattawan Yarbawa ta yabawa shugaba Buhari kan yarda da 'ya'yansu a nadin da yayi

- Sun kuma soki wani bangare na nadin da cewa ya kamata a dama da Inyamurai a nadin da yayi

- Dattawan sun bukaci shugaba Buhari da ya baiwa kowace kabila dama a fadin Najeriya

Wasu dattawa daga yankin Kudu maso Yamma a ranar Talata sun yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari kan nadin daya daga cikin ’ya’yansu a matsayin Babban Hafsan Sojin Sama, Daily Trust ta ruwaito.

Dattawan, a karkashin inuwar taron kungiyar dattawan Yarbawa, sun ce karimcin da shugaban ya nuna ya nuna matukar amincewarsa da Kudu maso Yamma don taimakawa gwamnatinsa ta bai wa ’yan Najeriya tsaron da ake matukar bukata kamar yadda ya yi alkawari.

Kodinetan kungiyar ta CCYE na kasa, Farfesa Olusegun Ajibola da Sakatariyar kungiyar ta kasa, Dr Catherine Adisa, sun bukaci ‘yan uwansu da su ba da gudummawar da shugaban ya yi musu ta hanyar tallafa wa gwamnatinsa don samun nasarar samar da zaman lafiya mai dorewa.

KU KARANTA: Ku shirya jure tsadar man fetur, Ministan mai ga 'yan Najeriya

Ya kamata Buhari ya dama da Inyamurai a nadin hafsoshi, in ji Yarbawa
Ya kamata Buhari ya dama da Inyamurai a nadin hafsoshi, in ji Yarbawa Hoto: Naija Views Now
Asali: UGC

Amma, sun nuna rashin jin dadinsu game da abin da suka kira da nuna wariya ga makwabtansu Inyamurai daga tawagar jami'an tsaro.

Sun ce wannan ya damesu kamar yadda ya faru a Kudu maso Gabas a karo na biyu tun daga 2015.

Sun bukaci Buhari ya duba nade-naden tare da daukar Kudu maso Gabas don adalci da daidaito.

Sun ce babu wata kabila ko yanki da ke da hannu dumu-dumu a aikin na Najeriya kamar sauran, suna rokon Buhari ya gyara "wannan kuskuren" ta yadda kowane bangare na kasar nan zai samu damar a dama dashi a Najeriya.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: WTO za ta nada Darakta-Janar a ranar Litinin mai zuwa

A wani labarin, Wani sabon rikici ya tunkaro jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, sakamakon wasu kalamai da aka ji sun fito daga bakin babban jigo a jam'iyyar Bola Ahmed Tinubu, BBC Hausa ta ruwaito.

Shi dai Tinubu wanda ake kyautata zaton zai nemi tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya ce aikin sabunta rijistar 'yan jam'iyyar dake gudana yanzu haka a jihohin Najeriya bashi da wani tasiri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.