Bayan an shawo kan ASUU, sauran Ma’aikatan Jami’a sun barke da danyen yajin-aiki

Bayan an shawo kan ASUU, sauran Ma’aikatan Jami’a sun barke da danyen yajin-aiki

- Kungiyoyin NASU da SSANU sun shiga yajin-aiki a Jami’o’in Gwamnati

- A dalilin haka an bar jami’o’i babu kula yayin da ake ta fama da COVID-19

- Ma’aikatan sun tafi na su yajin-aikin ne bayan kungiyar malamai ta dawo

Kungiyar manyan ma’aikata na jami’a na SSANU, sun yi kira ga iyaye da dalibai su fahimci dalilinsu na tafiya yajin-aiki a jami’o’in gwamnati.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, kungiyar SSANU ta roki al’umma su fahimci cewa ba da wani mugun nufi su ka shiga yajin-aiki a makon jiya ba.

SSANU ta ma bukaci iyaye da ‘yan makaranta su yi wa gwamnatin tarayya magana domin su amsa bukatun da su ka gabatar, wanda ya kai ga yajin.

Kungiyar ta ce ta fahimci cewa ma’aikatanta da kansu, ba su sha’awar yawan yajin-aikin da ake yi, amma SSANU ta ce rufe jami’o’in ya zama mata dole.

KU KARANTA: Shugaban kasa ya bada umarni ayi maza-maza a murkushe B/Haram

Shugaban kungiyar SSANU na kasa, Mohammed Haruna Ibrahim, ya ce saba alkawarin da gwamnati ta ke yi, ya sa ake tafiya yajin-aiki a kasar.

Malam Mohammed Haruna Ibrahim ya fadi wannan ne a wata hira da jaridar Daily Trust ta yi da shi.

Shugaban na SSANU ya ce sun tafi yajin-aiki ne domin su ceci ‘yan makaranta. “Mu na kokarin shawo kan lamarin ne. Mu na ba ‘Yan Najeriya hakuri.”

“Babu iyayen da zai zo ya tura yaronsa karatu zuwa jami’a, sai ya ga ya dawo gida saboda yajin-aiki a sakamakon tabarbarewar da abubuwa su ka yi."

Bayan an shawo kan ASUU, sauran Ma’aikatan Jami’a sun barke da danyen yajin-aiki
Ma’aikatan Jami’a su na zanga-zanga Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

KU KARANTA: A bude masallacin Sheikh Kabara idan ya yarda ya tuba - MURIC

A wani rahoton, mun ji cewa wannan sabon yajin aiki da SSANU da NASU su ke yi ya jawo cikas wajen karatun ‘yan makarana a wasu jami’o’in kasar.

Tun kwanaki ku ka ji cewa ma’aikatan jami’an gwamnatin wadanda ba su koyar wa sun gargadi gwamnati game da alawus din da za ta biya ma'aikata.

Kungiyoyin SSANU, NASU da NAAT na malaman fasaha da sauran ma’aikata jami’o’i su na kukan cewa akwai rashin adalci wajen ake rabon wannan kudi.

A dalilin haka ne kungiyoyin su ka umarci dukkan mambobinsu dake jami'o'in gwamnati su yi yaji.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel